Dakarun Sojin Amurka da ke Iraq da Syria sun fuskanci hare hare sau 38 a cikin makonni ukun da suka gabata, wannan dai wani mataki ne na goyon baya ga al'ummar Falasɗinu.
Ko a ranar talata 7 ga watan da muke ciki na Nuwamba sojojin Amurka da ke yankin Kurdistan sun bada rahoton cewa an hari sansanin su da ke Erbil mabanbantan hare hare har biyu inda aka samu fashewar bama bamai har uku da jirage marasa matuƙa suka jefa a sansanin.
Hakan kuma wani jirgin maras matuƙi ya ƙara jefa wani makamin duk a ranar sai dai wannan bai tashi ba.
Wata majiya ta bayyana ma kafar yaɗa labarai ta Shafaq cewa anji shawagin jirage marasa matuƙa lokacin da suka kawo hari sansanin sojin dake kusa da Filin tashin jiragen sama na Erbil da misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar 7 ga watan na Nuwamba.
Majiyar ta ƙara da cewa yayin wannan hare sojojin sun kunna Alarm a sansanin, sai dai zuwa haɗa rahoton ba a samun bayanan ɓarnar da makaman na ƴan gwagwarmaya suka yi ba a sansanin.
A sanadiyyar waɗannan hare hare sai da aka dakatar da tashin jirage a filin tashin jiragen na Erbil dake kusa da sansanin.
Bangarorin na ƴan gwagwarmayar ta Iraq sun tsananta hare hare a sansanonin sojin na Amurka ne domin nuna goyon bayan su ga al'ummar Falasɗinu.
Wannan harin na Erbil ya biyo bayan kwana ɗaya ne tak da kai hare hare sansanin sojin Amurka dake Ain al-Asad dake yankin Anbar a cikin ƙasar ta Iraqi da kuma sansanin Tel Baydar da Al-Tanf dake arewa maso gabashin ƙasar Syria, kamar yadda jaridar Rudaw ta wallafa a ranar 7 ga Nuwamba.
Ƴan gwagwarmayar sun bayyana cewa hare haren sun kai ga hadafin su.
Wannan dai shine karon farko ƴan gwagwarmayar suka hari sansanoni 4 a rana ɗaya.
Mai magana da yawun fadar tsaron Amurka (Pentagon) Birgediya Janar Pat Ryder ya bayyana wa manema labarai cewa an hari sojojin su har sau 38, sau 20 a Iraqi, sau 18 a Syria daga 17 ga watan Oktoba.
Ya bayyana cewa sojojin su 45 suka samu raunuka, wasu kuma sun samu matsalar ƙwaƙwalwa.
Kar ku manta dai cewa wannan harin na ƙarshe 7 ga wata ya zo ne bayan kwana ɗaya da zuwan sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ƙasar ta Iraqi.
Kafin zuwan Blinken ƙungiyar Kataeb Hizbullah dake Iraqi ta yi ma shi barazana wanda hakan ya tilasta shi shiga Iraqin cikin dare inda ya sauka tashar jiragen sama ta Baghdad sanye da rigar kariya daga harsashi (Bullet Proof).
Maƙasudin zuwan Blinken Iraqi shine tattaunawa da Firaministan ƙasar ta Iraqi domin a dakatar da hare haren ƴan gwagwarmayar kan sojojin na Amurka.