Daga - Mahadi Tukur Almizan
Wani ɗalibin jami'ar Tafawa Ɓalewa University (ATBU) dake jihar Bauchi ya shaƙi Iskar ƴanci bayan kwashe sati biyu a hannun masu garkuwa da mutane.
Ɗalibin mai suna Sama'ila yana karatun Civil Engineering ne a jami'ar ta ATBU, an yi garkuwa da shi ne a sati biyu da suka gabata a Gubi Campus dake jami'ar kamar yadda jaridar DailyPost ta ruwaito.
An ƙwamushe ɗalibin ne a ranar Lahadin sati biyun da suka gabata, inda daga baya masu garkuwa da mutanen suka nemi a basu zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan 10, sai dai daga bisani an daidaita akan Naira Miliyan 3.
Sai dai kuma shugaban sashen yaɗa labarai na jami'ar ya bayyana cewa bashi da masaniya akan faruwar lamarin, hakanan na shugaban rundunar ƴan sandan jihar SP Ahmad Wakili ya bayyana cewa ba a kawo masu rahoton faruwar lamarin ba.
✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update