Daga Wakilinmu:
_Auwal M. Tukur (Abu Ruhullah)_
Daruruwan al'umma musulmi ne, suka bayyana a masallacin Juma'a na sabuwar kasuwar garin Babban Rami, a yau juma'a 3/11/2023. Domin sake jaddada goyon bayansu ga al'ummar kasar Palestinu.
Lamarin ya faru jim kaɗan da idar da Sallar Juma'a a masallacin aka jiyo muryoyin al'umma musulmi almajiran Shaikh Zakzkay (H), suna ƙwalla salatin ga Manzon da iyalan gidansa tsarkaka. Tare da daga postoci, da kabbarori, hade da kira “Free Free Palestine."
A dai dai lokacin da yake jawabi, domin bayyana halin da kasar Palestinu suke ciki, wakilin yan uwa almajiran Shaikh Zakzkay na garin Malam Muhammad Tukur. Ya yi kira ga al'ummar kasar da su zama shaida cewa; “mu almajiran Sayyid Zakzaky (H), Muna tare da yan uwan mu musulmi na kasar palestinu.”
Bayan kammala takaicen jawabin sa a masallacin aka hau sahu domin yin muzaharar nuna goyon baya ga al'ummar kasar Palestinu.
Maza da mata, suka shiga sahun jerin gwanon, domin nuna goyon bayansu ga mutane kasar Palestinu.
Muzaharar wacce ta ratso tsakiyar garin, domin bayyanawa al'umma halin da mutanen Palestinu suke ciki. Inda mutane garin da dama ne suka fito a yayin da muzaharar ke wucewa.
An yi an kammala lafiya, tare da kona tutar haramtacciyar kasar Isra'ila. Da yin kashe di ga Yahudawan duniya, akan dole su kyale kasar Palestinu.
3th November, 2023.