Cikin daren jiya Juma'a Babban ɗan Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi, Shaikh Ibrahim Usman Bauchi tare da tawagar shi sun ziyarci Shaikh Yakub Yahya Katsina a markazin ’yan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) na garin Katsina .
A yayin ziyayar Shaikh Yakub Yahya Katsina ya nuna jin daɗin sosai akan wannan ziyarar ta musamman da suka kawo mashi.
An gaggaisa da juna, sannan an ƙarfafa juna akan muhimmacin haɗin kan musulmi, tare da gabatar da Addu'a ta musamman ga alummar Falasɗinawa.
Daga ƙarshe Shaikh Yakub Yahya Katsina ya bayar da kyauta ta musamman ga shehin malamin, sannan akayi Addu'a akayi banƙwana.
#SyykFacebookPage
04/11/2023.
Tags:
Daga marubata