Daga - Mahadi Tukur Almizan.
Ɓangaren mayaƙa daga ƙungiyoyin gwagwarmaya na Iraƙi da Syria suna cigaba da ɗanɗama sojojin Amurka dake yankin kuɗar su.
Wannan dai wani mataki ne na goyon bayan al'ummar Palasɗinu da Isra'ila ke kashewa a kowace rana tun bayan ƙaddamar da Operation ɗin "Al-Aqsa Flood" da ƙungiyar Hamas tayi.
A shekaran jiya juma'a da dare ƴan gwagwarmayar sun harba makamai zuwa wasu sansanonin sojin Amurka dake yankin Deir Ezzor dake Syria, wannan yanki na Deir Ezzor dai yana ƙarƙashin mulkin ƴan tada ƙayar baya masu adawa da gwamnatin shugaba Bashar Asad ne da ake kira "Syrian Democratic Forces" (SDF) waɗanda Amurka ke mara ma baya.
Ƙungiyar "Islamic Resistance In Iraq" (IRI) ta fito ta bayyana cewa ita ce takai hari a sansanin Al-shaddadi da ke kudancin birnin Hasakah ta ƙasar Syria.
Hakanan kuma an samu rahotan cewa anji fashewar abubuwa a sansanin Amurka dake Kharab Al-jir dake arewa maso gabashin Hasakah.
A nasu ɓangaren suma mayaƙan ƙabilun Larabawan Syria waɗanda tun watan Agustan da ya gabata suke ta yaƙar mayaƙan da Amurka ke mara ma baya na daga ƙabilun ƙurdawa, sun kai hare hare mabanbanta a kan mayaƙan SDF a Deir Ezzor da garuruwan Al-Tayyana, Dhiban, Al-Jaabi,Al-Bahra da Hajin.
Wata majiya ta bayyana ma jaridar Sputnik cewa ana kai hare hare duk da kasancewar jirage marasa matuƙa na Amurka na shawagi (Drones) harma da Helicopters a yankin, wannan dai ya nuna cewa waɗannan mayaƙa na ƙabilun Larabawan Syria sam sam basa shakkar Amurka da ƴan kanzaginta.
A daidai lokacin da ake kai hare hare kan sojojin Amurka a Syria, mayaƙan Ƙungiyar IRI sun bayyana cewa sune suka kai hari sansanin sojin Amurka Al-Harir wanda ke nisan kilomita 45 a arewacin tashar jiragen sama ta Erbil dake Arewacin Iraƙi.
Hakanan kuma a karon farko a jiya juma'a ƴan gwagwarmayar na Iraƙi sun kai ma Isra'ila hari a Kudancin birnin Eliat.
Idan baku manta ba dai kudancin birnin na Eliat ne mayaƙan Ansarulla na Yemen suka kai hari a satin da ya gabata.
✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update.
Allah ta'alah ya Qara basu nasara akan maqiya Allah da gangan
ReplyDelete