AN GUDANAR DA JANAZAR MUTANE BIYU DA JAMI'AN TSARO SUKA KASHE A GARIN KADUNA,

 


Daga- KADUNA PRESS ✍️


Da Safiyar Yau Jumu'a Aka Gudanar Da Janazar Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky (H) Mutum Biyu Da Jami'an Tsaro Suka Kashe Lokacin Muzaharar Nuna Goyon Bayan Al'ummar Palestine A Garin Kaduna Jiya Alhamis.


An Gabatar Da Janazar Ne A Fudiyya Rimi Rigasa Kaduna Inda Janazar Ta Samu Halartar Dubban Yan uwa Maza Da Mata Harda Mutanen Gari.


Jiya Alhamis Ne Dai Jami'an Tsaro Suka Kashe Mutane Biyu Almajiran Sheikh Zakzaky (H) Saboda Sun Fito Nuna Goyon Bayan Al'ummar Palestine Sannan Suka Sashe Wasu Mutane Biyu Daban.


Bin Muhammad

-Kaduna Press

-2022-11-17✍️

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post