An Buɗa Sabon Masallacin Juma'a A Jahar Edo State Benin City, Malam Ya'u Abubakar Garu Shi Ne Ya Zoma Sabon Lima

 





Daga -Bin Salihu Garu


Yau juma'a 27/11/2024 yan'uwa musulmi yan ɗariƙar tujjaniyya na garin Benin city sun buɗa sabon masallacin juma'a a unguwar magorawa moto park Wanda kuma malam Ya'u Sahabi Abubakar Garu ya zamo banban limamin masallacin, 


Dama dai shi wannan masallacin ya daɗe ana yin Salli bayar na yini a cikinsa sai Yau aka mai da shi masallaci juma'a mai cikakken ikon, manya-manyan malamai daga cikin garin Benin city sun halarci sallar juma'a a masallaci da bukin ƙaddamar shi masallaci ya zamo na sallar juma'a, bayan da malam Ya'u Abubakar ya gabatar da sallar juma'a an kuma yi addu'o'i na ganin ci gaban wannan abin alheri da al'ummar musulmi su ka samar wa kansu. An kuma yi wa shi malam Ya'u Abubakar addu'ar fatan Allah ta'ala ya tayi shi riƙo da jagoranci wannan masallacin da al'ummar da ya ke jagoranta


Ga Wasu hoton da muka ɗauko.









Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post