Amurka Tana Ƙaryar Ƙoƙarin Dakatar Da Isra'ila Daga Kai Hare Hare Gaza - Cewar ministan harkokin wajen Iran

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan


An labarto cewa Amurka na tattauna akan tsagaita wuta a Gaza da wasu shugabanni a yankin gabas ta tsakiya.


Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian ya bayyana cewa a makon da ya gabata Amurka na kiran a tsagaita wuta a Gaza ai dai ba da gaske suke ba.


Ya bayyana cewa "Amurka na neman a tsagaita wuta a Gaza amma a Social Media.


"Mun ji saƙon ku amma ƙarya kuke domin kuke kula da wannan yaƙin kan al'ummar Gaza da West Bank a Falasɗin, dan haka ku daina wannan munafurcin da kisan kiyashi kan al'ummar Gaza".


Domin kuwa a ranar 4 ga watan Nuwamba Anthony Blinken ya bayyana cewa " A mahangar mu idan aka tsagaita wuta hakan zai baiwa Hamas damar ƙara shiri da kuma sabunta hare hare.


Wannan shine dalilin da yasa Abdollahian ya ce Amurka ƙarya suke kan maganar tsagaita wuta da suke tayi a Social Media, domin a ƙarƙashin ƙasa suna cigaba da taimakon Isra'ila tana kashe Palasɗinawa.


✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post