Amurka Ke Ɓata Ma Kanta Suna Da Kanta - Kalaman Turkiyya Ga Amurka


 

Daga - Mahadi Tukur Almizan.


An labarto cewa ministan harkokin wajen Turkiyya ya faɗi ma takwaran sa na Amurka cewa Amurka tana zubar da mutuncin ta a idon duniya sakamakon goyon bayan ta'addancin Isra'ila a Gaza.


Ministan harkokin wajen na Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana ma Anthony Blinken waɗannan kalamai ne a lokacin ganawar su a ranar 6 ga wannan wata na Nuwamban da muke ciki.


A lokacin ganawar Fidan yayi maganganu ɓaro ɓaro dangane da yadda ake kallon Amurka da ra'ayoyin jama'a a yankin na Gabas ta tsakiya da ma duk duniya kamar yadda jaridar ƙasar ta Turkiyya "Hurriyet" ta labarto a ranar 7 ga watan Nuwamba.


Fidan ya bayyana cewa Amurka ta ɓata sunan ta a yankin da duk duniya, domin ana kallon Amurka a matsayin wadda ke da alhakin dukkanin hare haren Isra'ila akan al'ummar Gaza, duka waɗannan kalaman da Fidan ya faɗi ma takwaran na sa na Amurka Anthony Blinken ne a cewar Jaridar ta Hurriyet.


Ministan ya yi bayani sosai ga Anthony Blinken kan abinda yake faruwa a Gaza inda ya yi nuni akan irin rayukan da Isra'ila ta kashe a Gaza na dubunnan ƙananan yara, da kuma kadarorin da ta rusa.


Ministan ya faɗi ma Blinken cewa "Kun jefa kowa cikin matsala" an labarto cewa a lokacin da Anthony Blinken yayi ƙoƙarin rungumar Fidan ya janye jikin sa bai bari ya rungume shi ba, hakan alamu ne da ke nuna irin rashin jin daɗin Turkiyya Ga siyasar Amurka kan wannan lamari.


An bayyana cewa babu wani taron manema labarai da akayi a tsakanin ministocin biyu ko wata takardar manema labarai bayan kammala ganawar.


✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post