Hizbullah sun rubutawa Hamas Wasika ranar jumma'a, jiya asabar 4/11/2023 suka basu amsa kamar haka:
“Bismillah Rahmanirrahim.
Zuwa ga 'yan uwan mu na Gwagwarmayar Musulunci a Lebanon. Mun samu Wasikarku, hakika ku yan uwa ne na gaske a gwagwarmaya da tirjiya a kan hanyar zuwa Kudus.
Muna baku amsa daga zuciyar Falasdin, a cikin baraguzai da bangwagori, da kurar yaƙi da gwagwarmaya da maƙiyin da ya riga ya fadi. A lokacin da ruhunan iyalanmu, 'yayanmu, matanmu da tsofaffinmu da Shahidanmu suke kewaye da mu.
Ya 'yan uwanmu hakika mun karya, kuma mun rusa wannan rundunar maƙiyin ta fadi, sannan mun nunawa duniya ta gane yadda wannan makiyin yake cikin mayen yaudarar kansa. Yadda yake da rauni fiye da yanar Gizo-gizo. A lokacin da ya koma ƙisan kiyashi ga mata da kananan yara ya kasa fuskantarmu.
Yau, jajircewarmu da juriyarmu da karfin imaninmu bashi da gami. Muna da Imanin nasara ba makawa mara girgiza. A wannan lokacin dakarunmu marasa tsoro muna gwabzawa mai tsanani da makiya, muna kone motocinsu masu sulke.
Jaramtar mayakanmu yana saka gashin makiya ya koma furfura, yadda rundunarsa take dauke tabbacin rukushi, muna sanya hatta jininsu ya daskare. Makiya suna komawa baya, suna arcewa don gudun dannonwar makayanmu.
Mun fuskanci makiya gaba da gaba a kewayen da ake kira wai 'Kududdufin Gaza'. Koda ya hangomu muna dannowa sai ya juya da gudu cikin makyarkyata ya arce a sukwane.
Yan uwanmu muna lura da ayyukanku a cikin nutsuwa da kokarinku ba gajiyawa. Jinanan Shahidanku wanda ya cakuda dana mu. Muna lura cikin ladabi da girmamawa, jarumtarku da karfin hali mara girgizawa, yadda maƙiyi yake kyarma cikin firgici saboda jajircewarku a yaƙi. Kun tabbata kune Jagororin yaƙin a ko da yaushe.
Nasara mai tabbata ce a sakamakon wannan yaƙin. Muna da Imanin cewa wannan shi ne farkon rushewar dandazon azzaluman sahyonawa. Muna addu'a ga Allah ubangiji ya nuna mana ranar da zamu yi sujuda tare a Masallacin Kudus. Mu yi farin ciki a nasarar da ya bamu. Insha Allah wannan ranar tana zuwa.
DAGA YAN UWAN KU. YAN GWAGWARMAYAR MUSULUNCI.”