Akwai Yiwuwar Isra'ila Ta Jefa Nukiliya Bam A Gaza - Ministan Isra'ila Amichai Eliyahu.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan.


Jaridar "The Times Of Israel, ta ruwaito wani ministan haramtacciyar ƙasar Isra'ila da ya fito daga jam'iyyar Otzma Yehudit ya bayyana cewa ɗaya daga cikin zaɓin da Isra'ila ke dashi a yaƙin da take da Gaza shine jefa Bam ɗin Nukiliya.


Ministan ya faɗi haka ne a lokacin da ake hira dashi a wani gidan Rediyo Kol Berama, a hirar ne aka tambaye shi cewa ko Isra'ila zata iya yin amfani da Nukiliya Bom a Gaza? Sai ministan ya bada amsa da cewa wannan ɗaya ne daga cikin zaɓin da Isra'ila ke da shi a wannan yaƙin.


Eliyahu ya ƙara da cewa babu wata maganar cewa wai babu abinda ya shafi fararen hula a wannan yaƙin, dan haka bai kamata a bari wani tallafi ya isa Gaza ba.


Ya kuma bayyana goyon bayan rage yawan al'ummar Palasɗinawa domin a gina matsugunan Yahudawa, inda ya ƙare da cewa  Palasɗinawa suna iya komawa tsibirin Teku ko Sahara su rayu acan.


Ya ƙara da cewa duk wani mai ɗaga tutar Palasɗinu ko tutar Hamas bai cancanci rayuwa ba a doron ƙasa, ya kamata a kashe shi.


Sai dai ƙungiyar Hamas ta mayar da martani dangane da kalaman na wannan minista inda ta bayyana cewa waɗannan kalaman na ɗaya daga cikin ministocin haramtacciyar ƙasar Isra'ila ya ƙara bayyana ta'addancin Isra'ila akan al'ummar Palasɗinu.


Madogara zaku iya duba shafin "The Times Of Israel"


✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post