Wanann bincike ne na wasu masana da kuma likitoci. dangane da macen da take jinin al'ada yar uwa ya kamata ace kinsan dasu domin kiyi kokarin kaurace masu a yayin da kike jinin Al'ada..
GASU KAMAR HAKA..👇👇👇
1_ Kada kiyi amfani da ruwan kankara ko ruwan sanyi a lokacin da kike Al ada, saboda amfani da ruwan kankara yakansa jini ya daskare a mahaifa bazaitaba fita gabaki daya ba, wanda bayan shekaru 5 xuwa goma yakan kawo ciwon Daji na Mahaifa.
2_ A lokacin Al ada, kada ki sakawa kanki shamfo, kowacce kala saboda a wannan lokaci kofar gashinki a bude take, kuma shigar Shampo kofar gashi, yana kawo ciwon kai mai tsanani.
3_ A lokacin Al ada, kada ki ci Gurji ma ana Cucumber saboda akwai sinadarai a jikinta wanda zai hana jinin ya fita gabadaya, wanda daga karshe zai iya kawo ciwon Daji na mahaifa.
4_ A lokacin Al ada, koda wasa kada ki yarda a daki cikinki, kuma ki kiyaye duk wani abu da zai daki cikinki, saboda dukan ciki a wannan lokacin, zai yiwa mahaifa rauni wanda daga karshe zai iya zama ciwon Daji kuma yana kawo aman jini a lokaci guda.
5_ Kada kiyi amfani da gishiri mai yawa, amfani da gishiri mai yawa yana kawo yawan zubar da jini, kuma yakansa ruwa ya taru a Mahaifa.
6_ Kada kiyi amfani da kwakwa a lokacin Al ada saboda tana tsananta alamomi.
7_ A lokacin al ada, kada kiyi amfani da Barasa dukda bincike ya nuna tana rage radadi a lokacin Al ada, to akwai matsaloli da yawa da zai iya kawowa mace, idan tana amfani dashi.
8_ A lokacin Al ada, kada ki taba barin Pad sama da awa 3 zuwa 4 a jikinki koda jini baya zuwa Sosai.
9_ A lokacin Al ada, Tabar sigari dukkanninmu mun sani, tabar sigari yana da illa ga lafiyar jikinmu, bayan haka bincike ya nuna yawan amfani dashi a lokacin Al ada tana saka alamomi suyi tsanani.