Daga - Mahadi Tukur Almizan.
Kimanin mutum 50 ne suka yi shahada a wani hari da haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta kai kan wani masallaci a jiya Laraba 15 ga watan Nuwamba kamar yadda kafar yaɗa labarai ta WAFA News Agency ta ruwaito.
Isra'ila ta kai wannan hari ne a masallacin dai dai lokacin da ya ke cike da Palasɗinawa Musulmi a yayin da ake sallar Jam'i a Masallacin na Ihya - Ussunnah.
Wannan dai ba shine karon farko da Isra'ila ta kai hari muhallin ibada ba, Isra'ila ta kai hare hare mabanbanta a Masallatai da Coci Coci tun daga fara wannan yaƙi.
Ko a ranar 20 ga watan Oktoban da ya gabata, haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta kai hari Masallacin Al-Omari da ke Jabalia, wanda wannan masallaci yana daga cikin manyan Masallatai a Palasɗinu.
Kafin wannan hari na Masallacin Al-Omari Isra'ila ta kai hari Cocin "Saint Porphyrios" dake Gaza, wannan Coci itace Coci ta uku a Coci mafi daɗewa a Duniya baki ɗaya.
A sakamakon wannan hari kan Coci ƙungiyar "World Council Of Churches" ta fitar da sanarwar Allah wadai da ta'addancin Isra'ila a Gaza, kuma ƙungiyar tayi kira ga al'ummar Duniya wajen baiwa asibitoci, makarantu da wuraren Ibada na Palasɗinawa kariya.
✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update
Ya Allah ka daukaka musulinci da musulmai,ka danne kafirci da kafirai da masu Goya masu baya,ya Allah.
ReplyDelete