Zikirin Allah A boye Shine Mafificin Zikiri Kuma mafi Girman Lada!!!

 



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @ 


MALA'IKA BA YA RUBUTA ZUNUBI KO LADA SAI ABINDA YAJI KO YA GANI


Ita kalmar zikiri tana iya daukar ma'anar ambato ko tunawa, kowanne daga cikinsu yana lada domin Allah yayi umarni game da haka. 


Ambato na nufin furuci ko a bayyane ko kuma wanda aka furta cikin zuciya wanda kunne ne ke iya ji ko kuma Allah. 


Shi kuwa tunawa abu ne wanda zai shafi nazarin umarni ko hanin Allah, wato ya zama mutum na dubi a zuciyarsa kan abinda Allah yace yayi ko ya hane shi. Dukkan wanda aka aikata cikin biyun nan akwai lada, amma wanda akayi shi cikin zuciya ya fi girman lada. 


Allah mai girma da daukaka na cewa :


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ"


" KUMA KA AMBACI UBANGIJINKA CIKIN RANKA KANA MAI QASQANTAR DA KAI KANA MAI JIN TSORO, KOMA BAYAN BAYYANAWA DAGA MAGANA DA SAFIYA DA MARECE. KADA KA KASANCE DAGA CIKIN GAFALALLU. "


Wannan aya na yi mana umarni ne kan ambaton sunanSa a lokacin asubahi da yammaci, amma ambato a boye ba wanda mutane za suji ba. Ambaton Allah kuwa ana yi ne ta hanyar kiran sunayenSu guda 99 wadanda Yace kyawawan sunaye ne mu kiraye Shi dasu. 


Rashin zama a wadannan lokuta biyu ana ambaton Allah gafala ne, kuka Allah ya gargade mu da kada mu kasance cikin gafalallu. 


المصدر : 7


An samo riwayoyi kan wannan aya kamar haka :



الرسول (صلى الله عليه وآله)- وَ اذْكُرْ رَبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعاً يَعْنِي مُسْتَكِيناً وَ خِيفَةً يَعْنِي خَوْفاً مِنْ عَذَابِهِ وَ دُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ يَعْنِي دُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقِرَاءَةِ.


Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa :


" KA AMBACI UBANGIJINKA KANA MAI QASQANTAR DA KAI. " Abin nufi kana mai nutsuwa. " DA KUMA TSORO " Abin nufi shine jin tsoron azabarSa. " KUMA KOMA BAYAN BAYYANAWA DAGA MAGANA " Ana nufin koma bayan bayyanawa daga karatu.


المصدر :  بحار الأنوار، ج82، ص76 - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج5، ص460



Wannan riwaya na fassara mana ma'anar wannan ayar ne da cewa tana nufin ambaton Allah ne a zuciya ba tare da an furta shi kan harshe ba. 



Riwaya ta gaba daga Imam Ali (A. S) cewa :


أمير المؤمنين (عليه السلام)- مَنْ ذَكَرَ اللَّهَ عَزَّ‌وَ‌جَلَّ فِي السِّرِّ فَقَدْ ذَكَرَ اللَّهَ كَثِيراً إِنَّ الْمُنَافِقِينَ كَانُوا يَذْكُرُونَ اللَّهَ عَلَانِيَةً وَ لَا يَذْكُرُونَهُ فِي السِّرِّ فَقَالَ اللَّهُ عَزَّ‌وَ‌جَلَّ يُراؤُنَ النَّاسَ وَ لا يَذْكُرُونَ اللهَ إِلَّا قَلِيلًا.



" DUK WANDA YA AMBACI ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA A BOYE, TO, HAQIQA YA AMBACI ALLAH DA YAWA. LALLE MUNAFUKAI SUN KASANCE SUNA AMBATON ALLAH A BAYYANE NE, KUMA BA SA AMBATONSA A 'BOYE. SHINE ALLAH (T) YACE :


" SUNA NUNAWA MUTANE, BA SA AMBATON ALLAH SAI 'DAN KADAN. "


المصدر :  الكافي، ج2، ص501/ نور الثقلين - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج5، ص460


Daga cikin abinda hadisin ke karantar damu shine ambaton Allah a boye shine mafi alkhairi da kuma yawan lada. Siffar Munafukai ita yawan bayyanar da aiki amma babu shi cikin zuciya, imma akwai to, qanqani. 


A riwayar Imam Baqir (A. S) kuma yana cewa :


الباقر (عليه السلام)- لَا يَكْتُبُ الْمَلَكُ إِلَّا مَا سَمِعَ وَ قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ وَ اذْكُرْ رَبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعاً وَ خِيفَةً فَلَا يَعْلَمُ ثَوَابَ ذَلِكَ الذِّكْرِ فِي نَفْسِ الرَّجُلِ غَيْرُ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ لِعَظَمَتِهِ.


" MALA'IKA BA YA RUBUTA (lada ko zunubin wani abu) FACE ABINDA YAJI. ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA CE :


" KUMA KA AMBACI UBANGIJINKA CIKIN ZUCIYARKA KANA MAI QAAQANTAR DA KAI DA KUMA TSORO. " (Imam yace) :


" BABU WANDA YASAN SAKAMAKON WANNAN ZIKIRI (da akayi shi boye) CIKIN ZUCIYA MUTUM FACE ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA, SABODA GIRMANSA. "

المصدر : 

 الكافي، ج2، ص502/ وسائل الشيعةًْ، ج7، ص163/ مستدرك الوسائل، ج5، ص299/ 

بحار الأنوار، ج5، ص322/ الزهد، ص53/ عدة الداعي، ص259/ نور الثقلين/ 

البرهان - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج5، ص460


Ma'ana zikirin Allah a boye shine mafificin zikiri wajen Allah, domin Shi yasan girmansa. Mala'ika bai san abinda ke cikin zuciya ba sai dai abinda idonsa zai gane masa ko kuma abinda kunnensa ya jiye masa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


     (08137925034)

     Baban humaid

16th October, 2023/  1st Rabi'us-Sani, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post