YAN UWA MUSULMI ALMAJIRAN SHAIKH ZAKZAKY SUN NUNA GOYON BAYANSU GA AL'UMMAR PALESTINE A GARIN BABBAN RAMI

 


©️M.N.N. Updates


Yau Juma'a 27/10/2023 Yan uwa Musulmi suka gudanar da muzaharar nuna goyon bayan su ga al'ummar kasar Palestine.


Jin kadan da idar da sallar juma'a yan uwan suka hau sahu masallacin juma'a dake sabuwar kasuwa. 



Suna tafe dauke da tutocin da manyan hotunan Shaikh Zakzkay, wadanda suke alamta nuna goyon baya ga raunanan kasar Palestine. 



Sun cigaba da tafiya cikin tsari da izza, suna tsinewa Haramtacciyar kasar Isra'ila, wacce take kashe raunanan kasar ta Palestine.


Yan uwan masa da mata ne suka yiwa babban titin zuwa Lagos tsinke. Domin nuna goyon bayan , da sanar da al'umma halin da mutanen Palestine suke ciki.



A bangare daya zaratan matasa ne suke jan tutar haramtacciyar kasar Isra'ila a kasa. Domin nuna adawa da kin jinin Isra'ila na irin ta'addanci da kisan gillar da suke yiwa al'umma musulmi daga Kiristocin kasar Palestine.


Anyi muzaharar lafiya an kammala lafiya. 


Allah ya kara tallafawa al'umma kasar Palestine.


Ga wasu daga hotunan da wakilin mu ya aiko mana da su.


Daga Auwal M. Tukur (Abu Ruhullah)

27, OCT, 2023.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post