WAI DA GASKE SABANIN AL'UMMAR ANNABI (S. A. W. W) RAHMA CE ???

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


AL'UMMA BA TA SABAWA HAR SAI TA QI BIN GASKIYA


Abinda babu kokonto ko sabani a kansa shine al'ummar larabawa tayi fice wajen sassabawa junansu wanda hakan ya janyo mummuniyar gaba wacce ta haifar da yaqe-yaqe a junansu. 


Abu na biyu bayan tauhidin da Annabi (S. A. W. W) ya kirawo su a kansa shine qoqarin hada kansu guri guda ta yadda soyayya da qaunar juna za ta dinke tsakaninsu, domin hakan shine cigaba da kuma fahimtar juna tare da zaman lafiya. Wannan hadin kan bai tsaya iya cikin larabawan Makkah ba, domin shine abu na farko da Annabi (S. A. W. W) ya shimfida tsakanin mutanen Makkah da Madinah yayin da yayi Hijra. 


Akwai riwayar da malamai ke yawan kawota cikin al'umma don tabbatar da da'awarsu ta rarraba kan al'ummar musulmi. Wannan riwaya kuwa ita ce wai Annabi (S. A. W. W) ya ce :


" SABANI TSAKANIN AL'UMMATA RAHMA CE. "


Wannan riwaya ta basu damar cin Karensu ba babbaka, domin kowa daga cikinsu na amfani da ita (riwayar) rarraba kan al'umma da sunan rahma. Lalle wannan qirqire ya saba da hankali ballantana ilimi, domin ba zai taba yiwuwa ace mutane su rarrabu da sunan sabanin fahimta sannan ace an sami cigaba ba, lalle cikin wannan sabani akwai wacce take gaskiya, kuma kamata yayi saura su dawo kanta sun dinke guri guda. 


Duk inda kaga an sami sabani kuma aka cigaba da tafiya a haka, to, gaskiya ce aka kauce mata.


Allah (S. W. A) na cewa :


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" وَلَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ تَفَرَّقُوا وَاخْتَلَفُوا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْبَيِّنَاتُ وَأُولَئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ."



" KUMA KADA KU KASANCE KAMAR WADANDA SUKA RARRABU KUMA SUKA SABA BAYAN HUJJOJI BAYYANANNU SUN ZO MUSU, WADANNAN AKWAI AZABA MAI GIRMA GARE SU. "


Wata rana Imam Ali (A. S) ya rubuta takarda zuwa ga Mu'awiyata cewa :


أمير المؤمنين (عليه السلام)- كَتَبَ إِلَى مُعَاوِيَة ... أَدْعُوكَ يَا مُعَاوِيَةُ إِلَى اللَّهِ وَ رَسُولِهِ وَ كِتَابِهِ وَ وَلِيِّ أَمْرِهِ الْحَكِيمِ مِنْ آلِ إِبْرَاهِيمَ (عليه السلام) وَ إِلَى الَّذِي أَقْرَرْتَ بِهِ زَعَمْتَ إِلَي اللَّهِ وَ الْوَفَاءِ بِعَهْدِهِ وَ مِيثاقَهُ الَّذِي واثَقَكُمْ بِهِ إِذْ قُلْتُمْ سَمِعْنا وَ أَطَعْنا وَ لا تَكُونُوا كَالَّذِينَ تَفَرَّقُوا وَ اخْتَلَفُوا مِنْ بَعْدِ ما جاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْياً بَيْنَهُمْ وَ لا تَكُونُوا كَالَّتِي نَقَضَتْ غَزْلَها مِنْ بَعْدِ قُوَّةٍ أَنْكاثاً تَتَّخِذُونَ أَيْمانَكُمْ دَخَلًا بَيْنَكُمْ أَنْ تَكُونَ أُمَّةٌ هِيَ أَرْبي مِنْ أُمَّةٍ فَنَحْنُ الْأُمَّةُ الْأَرْبَي."


" INA KIRANKA YAA MU'AWIYYATA ZUWA GA ALLAH DA MANZONSA DA KUMA LITTAFINSA DA JIBINTAR WALIYYIN AL'AMARINSA MAI HIKIMA DAGA IYALAN IBRAHIM (A. S), DA KUMA ZUWA GA WANDA  KUKA TABBATAR DASHI.  KUN RIYA (dau alqawari) ZUWA GA ALLAH DA KUMA CIKA ALQAWARINSA DA (wannan) ALQAWARIN NASA WANDA A KAYI MUKU ALQAWARI DASHI YAYIN DA KUKA CE : " MUNJI KUMA MUN BI. "


KADA KU KASANCE KAMAR WADANDA SUKA RARRABA KUMA SUKA SASSABA BAYAN ILIMI YA ZO MUSU, SABODA ZALUNCI DAKE TSAKANINSU. KUMA KADA KU KASANCE KAMAR WACCE TA WARWARE TUFKARTA BAYAN TA YI QARQI (sai kuma) TA WARWARETA. KUMA RIQON RANTSUWARKU A MATSAYIN KAMBU (wanda zai hana aikata abin kirki) A TSAKANINKU, KU HA'INCI AL'UMMA WACCE ITA CE MAFI ALBARKA DAGA AL'UMMA. TO, MUNE (wannan) AL'UMMA MAFI ALBARKA. "


المصدر :  بحارالأنوار، ج33، ص138 - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج2، ص728


Wannan gargadi ne Imam Ali (A. S) ya yiwa Mu'awiyata Bn Abu Sufyan, domin dukkan abinda suka yiwa Imam Ali (A. S) ba wai sun yi shi bisa jahilci ko rashin sani bane, a'a, bisa ilimi suka aikata hakan, domin sun san matsayinsa sai dai jayayya da wannan matsayi don sabawa Manzon Allah (S. A. W. W). Amma sai malaman baya suka ce abinda Mu'awiyata yayi sabanin fahimta (IJTIHADI) ne, saboda haka babu mai kuskure a tsakaninsu. 


A wani guri kuma Allah ya qara da cewa :


" وَمَا تَفَرَّقُوا إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ وَلَوْلَا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ إِلَى أَجَلٍ مُّسَمًّى لَّقُضِيَ بَيْنَهُمْ وَإِنَّ الَّذِينَ أُورِثُوا الْكِتَابَ مِن بَعْدِهِمْ لَفِي شَكٍّ مِّنْهُ مُرِيبٍ."



" KUMA BASU RARRABA BA HAR SAI BAYAN ILIMI YA ZO MUSU SABODA ZALUNCI A TSAKANINSU. DA BA DON WATA KALMA DATA GABATA DAGA UBANGIJINKA BA ZUWA WANI AJALI (lokaci) AMBATACCE BA, HAQIQA  DA ANYI HUKUNCI TSAKANINSU. KUMA LALLE WADANDA AKA GADAR MUSU DA LITTAFI A BAYANSU SUNA CIKIN KOKONTO MAI SANYA SHAKKU DAGA GARE SHI. "


Haka ita ma wannan aya na tabbatar mana ne da cewa lalle sabani ko rarrabuwar kai ba haka kawai ne take faruwa ba, lalle bisa ilimi ake yinsa saboda wasu dalilai na masu kawo wannan sabani/rarraba. To, ta yaya za ace sabani ya taba zama rahma in ba musiba ba  ?


علي بن ابراهيم القمي (رحمه الله)- قَوْلُهُ تَعَالَى وَ ما تَفَرَّقُوا إِلَّا مِنْ بَعْدِ ما جاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْياً بَيْنَهُمْ قَالَ لَمْ يَتَفَرَّقُوا بِجَهْلٍ وَ لَكِنَّهُمْ تَفَرَّقُوا لَمَّا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ وَ عَرَفُوهُ فَحَسَدَ بَعْضُهُمْ بَعْضاً وَ بَغَي بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْضٍ لَمَّا رَأَوْا مِنْ تَفَاضُلِ أَمِيرِالْمُؤْمِنِينَ (عليه السلام) بِأَمْرِ اللَّهِ فَتَفَرَّقُوا فِي الْمَذَاهِبِ وَ أَخَذُوا بِالْآرَاءِ وَ الْأَهْوَاءِ ثُمَّ قَالَ عزَّوَجَلَّ وَ لَوْ لا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِنْ رَبِّكَ إِلي أَجَلٍ مُسَمًّي لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ قَالَ لَوْ لَا أَنَّ اللَّهَ قَدْ قَدَّرَ ذَلِكَ أَنْ يَكُونَ فِي التَّقْدِيرِ الْأَوَّلِ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ إِذَا اخْتَلَفُوا وَ أَهْلَكَهُمْ وَ لَمْ يُنْظِرْهُمْ وَ لَكِنْ أَخَّرَهُمْ إِلَى أَجَلٍ مُسَمًّي الْمَقْدُورِ وَ إِنَّ الَّذِينَ أُورِثُوا الْكِتابَ مِنْ بَعْدِهِمْ لَفِي شَكٍّ مِنْهُ مُرِيبٍ كِنَايَةٌ عَنِ الَّذِينَ نَقَضُوا أَمْرَ رسول الله (صلى الله عليه و آله)."


Ya zo cikin Tafsir na Qummy Allah yayi masa rahma cikin fadinSa (A. W. A)  :


" KUMA BASU RARRABA BA FACE BAYAN ILIMI YA ZO MUSU BISA ZALUNCI TSAKANINSU. " Yace :


" Ba wai sun rarrabu bisa jahilci bane, sai dai su sun rarrabu ne yayin da ilimi yazo musu, kuma suka san shi, sai sashensu yayi yiwa sashe hassada kuma sashensu ya qetare iyaka akan sashe yayin da su kaga fifikon shugaban muminai (A. S) a kansu na al'amarin Allah, sai suka rarrabu cikin Mazhabobi kuma su kayi riqo da ra'ayoyi da bin son zuciya. Sa'an nan mai girma da daukaka yace :


" DA BA DON WATA KALMA DATA GABATA DAGA UBANGIJINKA BA ZUWA WANI LOKACI AMBATACCE, TO,  DA ANYI HUKUNCI TSAKANINSU. "


Yace : " Da ba don Allah ya qaddara haka ba don ya kasance cikin qaddara  ta farko ba, to, da ya yi hukunci a tsakaninsu yayin da suka sassaba, kuma ya halakar dasu ba zai saurara musu ba, sai dai ya jinkirta musu ne zuwa wani lokaci ambatacce wanda aka qaddara shi. " KUMA LALLE WADANDA AKA gadar MUSU DA LITTAFI A BAYANSU  SUNA CIKIN KOKONTO MAI SANYA SHAKKU DAGA GARE SHI . " Wannan kinaya ce ga wadanda suka warware umarnin Manzon Allah (S. A. W. W) (da ya nasabta Imam Ali, har su kayi bai'a a lokacin, amma sai suka warware shi bayan wafatinsa (S. A. W. W). 



المصدر :  بحارالأنوار، ج9، ص234 - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج13، ص590


Saboda haka lalle maganar sabanin al'umma rahma ce ya ci karo da ayoyin Al-Qur'ani, kuma yayi hannun riga da aikin Manzon Allah (S. A. W. W), domin shi a kullum umarni yake yi kan hada kai da fahimtar juna don a hada qarfi a yiwa addinin muslimci aiki. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


         (08137925034)

Baban humaid Mnnu//Ng0027

21st October, 2023/ 6th Rabi'us-Sani, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post