Sojojin Nigeria zasu aiwatar da bincike kan zargin rashin ba su isasshen abinci'


Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta ce "za ta gudanar da bincike nan take a kan ƙorafe-ƙorafen" rashin bai wa sojoji da ke yaƙi da Boko Haram isasshen abinci.Hedkwatar sojojin ƙasan ta ce hankalinta ya kai kan ƙorafe-ƙorafen cewa dakarunta da ke fagen yaƙi da Boko Haram, ba sa samun ingantaccen abinci.

Wani sojan Najeriya da muka zanta da shi ta wayar tarho daga arewa maso gabashin Najeriya, inda suke yaƙi da 'yan Boko Haram, ya ce matsalar rashin ingantaccen abinci da suke ciki, da wuya a iya misalta ta.“Mun sha fita zuwa daji, ba tare da mun ci wani abin kirki ba. Matsaloli da muke fuskanta ba su da adadi,” in ji sojan wanda ya nemi a sakaya sunansa.Ya yi zargin cewa abincin da ake ba su bai taka kara ya karya ba, kafin su fita bakin fama. Sai dai a cikin sanarwa da mai magana da yawunta, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu ya fitar ranar Talata, rundunar sojin ƙasan Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike nan take a kan zarge-zargen domin gano haƙikanin gaskiyar abubuwan da ke faruwa.

Sanarwar ta ambato babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja na cewa: “Muna son tabbatarwa dukkan dakarunmu da kuma al’umma cewa za mu yi cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.Shi dai sojan da muka zanta da shi ya bayyana mana cewa: “Akwai rundunoni daban-daban a inda muke (aiki), wataƙila abin da ake ba mu a wajen da muke, ba haka yake a sauran wurare ba."Wani lokaci akan mutum ya ci abincin da ake dafawa, gwara an ba ka naira ɗari biyu ka sayi burodi ko cincin,” in ji shi.“Teba ake dafa mana mu ci, idan za mu fita aiki. Wani lokacin ma sai garin ya lalace. Ta yaya za a ba ka wannan abinci sannan a ce ka je ka yi yaƙi da Boko Haram?”

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post