SHEKARU BIYU (2) DA WATA UKU (3) !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


WANNE HALI SHEIKH ABDUL-JABBAR KE CIKI  ?


Ranar 18th Zul-Hijjah, 1442 ita ce ranar da hukumar zalunci ta Muhammadu Buhari ta saki Sayyid Ibraheem Zakzaky  (H) daga tsarewar da tayi masa na tsahon shekaru biyar da rabi (5.5).


Wannan rana ta zama rana ta farin ciki biyu (2) ga mabiya tafarkin Ahlul-Bait (A. S) qarqashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H). Dalilin wannan farin ciki guda biyu shine, ita ce ranar da Annabi (S. A. W. W) ya nasabta Imam Ali (A. S) a matsayin Halifan farko bayansa. Wannan al'amari kuwa ya faru ne ranar 18th Zul-Hijjah, 10 (B. H) a wani guri da ake kira Ghadeer kan hanyarsa (S. A. W. W) ta dawowa daga Makkah. 


A daidai wannan rana da mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah (S. A. W. W) ke murnar zagayowar ranar sai ya zama Gwamnatin zalunci ta Muhammadu Buhari ta sako Sayyid Zakzaky (H) daga tsarewar zaluncin da take masa. Wadannan abubuwa biyu sun zama abin farin ciki wadanda yasa mabiyan Sheikh Ibraheem El-Zakzaky su kayi walima biyu lokaci guda. 


SHEIKH ABDUL-JABBAR 


Da shike duk tsarin zaluncin iri daya ne ko nace abu guda né domin hadafinsu daya ne, masu daukar nawin qasa daya ce . Su suke tsarawa da daukar nawwi, sai kuma su bawa yaransu na kowacce qasar da suke so su aiwatar musu abinda suke so. 


A lokacin da Yahudu suka gama tsara abinda suke so a yiwa Sheikh Abdul-Jabbar suka miqa abin zuwa ga Saudiyyah, sai su kuma suka bawa Gwamnan Kano wannan aiki tare da nuna masa hanyoyin da zai bi kafin aiwatar da wannan aiki. 


Salon da Gwamnatin Kano ta dauka shine bada kwangila ga wasu manyan malamai na 'Dariqar Tijjaniyya da Qadiriyya da Izala da kuma 'yan Salafiyya cewa su san  hanyar da za su bi su bata Sheikh Abdul-Jabbar tare da cusa qiyayyarsa cikin zukatan mutane ta yadda duk abinda ya faru a kansa za ace daidai ne.


Bayan Gwamnatin tarayya data jihar Kano ta gama tsara abinda za tayi sai ta sanya ranar 18th ga Zul-Hijjah 1442 ta zama ranar yanke hukuncin shari'ar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky (H) data Sheikh Abdul-Jabbar (H). Da aka zo yanke hukunci sai aka ce Sayyid Zakzaky (H) ba shi da laifin komai, saboda haka kotu ta sake shi. Shi kuma Sheikh Abdul-Jabbar tace aikinsa ya cancanci a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya (Hanging).


Wannan hukunci na koto kan Sayyid Zakzaky (H) ya farantawa muminai rai, sannan hukuncin da aka yanke kan Sheikh Abdul-Jabbar ya baqantawa muminai rai. 


Su kuwa fajirai maqiya muslimci sunyi baqin ciki da sakin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), kuma sunyi farin ciki da hukuncin da aka yanke kan Sheikh Abdul-Jabbar. 


Manyan almajiran Sayyid Zakzaky (H) da qanana sun nuna rashin goyon bayansu ga wannan hukunci na zalunci tare da bayyana hujjojinsu na cewa zalunci, kuma irin haka aka yiwa Sayyid Zakzaky (H) wanda wasu ke ganin daidai ne. 


LAIFIN BA A WAJEN GANDUJE BANE 


Abin nufi anan shine, shi dai Ganduje yayi aikin kudi ne kuma an biya shi ladansa, domin shi aikin gyaran duniyarsa yake yi ba lahira ba.


Almajiran Sheikh Abdul-Jabbar sunyi iya abinda za su iya wajen tabbatarwa al'umma cewa Sheikh Abdul-Jabbar fa zaluntarsa akayi, amma abinda ake fada a kansa wanda ya jefa shi halin da yake ciki qarya ne, domin gaskiyar magana cikin da ya daukawa kansa shine daukaka darajar Manzon Allah (S. A. W. W) ta hanyar warware hadisan qarya da ake alaqanta su gare shi, wanda hakan ya janyo Yahudawa ke amfani da wadannan riwayoyi suna aibanta Manzon Allah (S. A. W. W). 


Almajiran Sheikh Abdul-Jabbar sun zaci alhakin tsarewa da fitar da Sheikh Abdul-Jabbar na hannun Ganduje ne, saboda haka su kayi alwashi fitowa qwansu da qwarqwatarsu suyi zabe don kayar da Ganduje. A fahimtarsu faruwar Ganduje da hawan sabon Gwamna shi zaiyi sanadin fitowar Sheikh Abdul-Jabbar. 


BABBAN ABINDA BASU FAHIMTA BA 


Shi fa kafirci da tsarinsa abu guda ne, tare suke tafiya ba sa rabuwa. Ba zai yiwu ace tsarin kafirci ne ke jagoranci sannan kuma ace adalci zai tafi a qarqashinsa ba.


A lura da kyau, da ace adalci na tafiya qarqashin tsarin kafirci da yawan canjin Gwamnati da ake yi da kunga adalci, domin kowanne mai neman mulki za kaji cikin kamfen nasa yana cewa ba a adalci, amma in har Allah yasa ya sami kujerar da yake nema zai yi adalci tare da bawa kowa haqqinsa, amma yana hawa sai kaji ana kuka dashi fiye da wanda ya sauka. 


ME YA HANA GWANATIN KANO SAKE SHEIKH ABDUL-JABBAR  ?


Anyi zaton hawan sabuwar Gwamnatin Kano za ta sake Sheikh Abdul-Jabbar, domin a tunanin mutane laifin na Ganduje ne. Sai ga shi tafiya ta soma nisa cikin sabuwar Gwamnati amma babu wata magana dake nuna cewa ana shirin sakin wannan Shehin malami mai tsoron Allah.


Duk wanda kaga ya sami babban mulki a wannan qasa sai da amincewar Yahudu da nasara, idan suna sonka za ka sami mulki, kuma ba za ka aikata wani abu cikin mulkinka sabanin abinda suke so ba. 


Na'am, ba cewa nake komai su suke tsarawa ba, a'a shugaba na da 'yancin aiwatar da wasu abubuwa masu muhimmanci ga al'umma, amma dai ba al'amarin addini wanda shine barazana gare su ba. 


Wannan murya ta Sheikh Abdul-Jabbar na daga cikin mafi girman abinda Yahudawa ke qi, domin tsarkake koyarwar muslimci shine izzar muslimcin. Saboda haka duk wanda ya hau mulki a jihar Kano ba zai iya sake Sheikh Abdul-Jabaar ba, sai dai in wadanda suka bada aikin né su kayi niyya, su kuwa ba sa kyakkyawar niyya sai dai qarfin ikon Allah kawai a kansu. 


ABINDA YA HAU KAN MABIYANSA 


Addu'ah malamin mumini ce, amma duk da sanin hakan bai sa Annabi (S. A. W. W) ya tsaya kan addu'ah kadai ba, dole sai da yayi gwagwarmaya da jikinsa da jininsa da dukiyarsa kafin aci nasara. 


Saboda haka ya kamata su riqa fitowa suna bayyana rashin amincewarsu na cigaba da wannan tsarewa ta zalunci kamar yadda mabiya Sayyid Zakzaky (H) suka riqa yi.


Bayan sakin da aka yiwa Sayyid Zakzaky (H) sai ya zama an kafa masa wani takunkumi wanda ba zai taba barinsa ya fita waje wajen neman magani ba.  Sanin muhimmancin fitowa ana nuna zaluncin azzaluma sai mabiyan nasa suka riqa fitowa kan Tituna gari-gari suna nuna rashin amincewarsu na cigaba da riqe masa Passport, ana kashe wasu ana jiwa wasu raunuka amma suka dake har burinsu ya cika. Yanzu haka su Sheikh Zakzaky (H) na shirye-shiryen fita qasar waje wajen neman magani. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

        (08137925034)

         Baban humaid

8th October, 2023/  23rd Rabi'u-Awwal, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post