بِسْمِ الله الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ بِأَنَّهُمْ ظُلِمُوا ۚ وَإِنَّ اللَّهَ عَلَىٰ نَصْرِهِمْ لَقَدِيرٌ
"An yi izni ga wadanda aka kashe saboda an zalunce su, kuma lallai hakika, Allah Mai ikon yi ne, a kan taimakonsu."
YA KU 'YAN UWA DA SHAWAGABANNI DA JAJIRTATTUN MATASA MASU ƘUMAJIN AIKI A CIKIN AN'UMMAR LARABAWA DA MUSULUNCI...!
A wannan lokaci mai albarka, wanda 'yan'uwanku mujahidai a Gaza suke gudanar gagarumi kuma muhimmin Yunƙuri na yaƙin neman 'yanci daga Mamaya, da izinin Allah. Yanzu haka sun yiwa makiya yahudawan sahyoniya, babban Rauni. Yahudawan da wadanda suka wuce Gona da Iri, cin mutunci da tozarci ga Massalin Qudus da wurare masu tsarki.
Suka wuce zurfafa wajen kisan mummuƙe da Korar ‘ya’yan Al’ummarmu ta Palastinu daga gidajensu da Garuruwansu. Kuma suke kokarin karya lagon mujahidanmu da daƙushe ikonsu na yakar 'Yan mamaya.
Amma duk da haka, al'umarmu mai 'Yanci da ƙin zalunci ta ƙi yarda, ta ƙi miƙa wuya, ta zabura ta bude sabon shafi na Izzah da Buwaya, ta hanyar yayyafa kasashenmu da aka mamaye da dubunnan makamai masu linzami, saman Gine-ginensu, da ke kewaye da Gaza.
Wannan zafin nama da dukar fari, ta Ɗimauta magauta ta basu mamaki, inda Mujahidai suka kwace iko da wuraren maƙiya yahudawan sahyoniya tare kawar da su, da tunkuɗe Sankensu. Hakan ya yi sanadin kashewa da Damƙe gommai, ko kuma muce Daruruwansu, duk wannan na faruwa ne a cikin kwamin da aka masa suna da "Ambaliyar Aqsa".
YA KU MATASA MASU TAWAYE...
A yau Gwagawarmaya ta canja sabon salo. Kuma abun da ke faruwa yanzu, wata Gaɓa ce (mai muhimmaci) wadda za ta sauya Ma'aunin Karfi da Iko, tun a yau da kuma bayan yau. A yau makiya yahudawan sahyoniya suka shelanta yaki a karon farko tun bayan shekara ta 1973 miladiyya, kuma a yau mun ga fushin Falasɗinawa da jaruntakar da suke da ita, inda suka iya tsayawa kan-kan-kan suna fuskantar girman kai na yahudawan sahyoniya suna halarto da faɗin Allah maɗaukaki:
“Ku shige su ta kofa, kuma idan kuka shige to ku ne masu rinjaye, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai.”
Mu a nan Alhamdulillah a natse muke, mun yi Imani da samun nasara daga Allah, kuma Allah ba zai wofintar da ayyukanmu ba. Ta yaya ko ba zai kasance tare da mu ba, Al'hali yankin Gaza ya zamo tsangayar Al'kur'ani..? Inda shaida taro mafi girma na mahaddata Littafin Allah, (kuma mujahidai) wadanda suke yin saukar Alkur’ani bila adadin a duk zama Ɗaya.
To yau wadannan Mahaddatan ne da kansu suka fita dominGwabzawa da makiya. Kar a manta Allah madaukaki yana cewa, game da cikawa bayi Al'kawalin samun galaba: “Ya ku wadanda suka yi imani, idan kuka taimaki Allah zai taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku”.
YA KU MATASAN AL'UMMARMU TA LARABAWA DA MUSULUNCI, YA KU BABBAR MALAƁARMU TA DABARUN YAƘI, YA KU BABBAR KARIYAR GWAGWARMAYAH MAI KARFI...!
Ku sani, yau ce ranar da aka haifeku dominta, ta taimakon al'ummar Falasɗnu da kuma dafawa gwagwarmayar da suke yi, kuma ba ma fatan waninku zai laɓe a bayan Dukiyarsa, ko Iyalinsa,ya kasa taimakon Addinin Allah. Tabbas yau ce ranar rarrabewa, ya kamata mu nuna wa Allah abin da ya dace daga gare mu, don haka ku gaze Dantse, ku ƙara Himma, ku tallafawa wurarenku ma su Tsarki, ku kare Mallacin Qudus, ku kawo masa Ɗauki. Allah shi ne majibincinmu, kuma makiyanmu ba su da wani majibinci.
Saboda nauyin hakki na shari'a da Mutuntaka, muna kiranku a kan aikata wasu abubuwa masu muhimmanci kamar haka:-
1. Wayarda kan sauran Matasa, ta hanyar Shirya taron gama gari a tsakanin matasan al'ummarmu na larabawa da na Musulunci. Da kuma fita Muzaharori nuna goyon baya ga Al'ummar Falasɗinu, da masallacin Ƙudus, domin nuna goyon baya ga gwagwarmaya. Lallai suna bukatar muryoyinku su isarwa Duniya sakonsu.
2. Yi wa mujahidan yankin Gaza da dukkan kasashenmu na Flasɗinawa Addu'ar neman samun nasara da tagomashi, kuma ya zama kiran tahajjud da addu'o'in da ya cika sararin samaniya, domin ya kuma firgita makiya Allah.
3. Matsin lamba ga gwamnatoci da Al'ummomin duniya ta dukkan hanyoyin da suka dace don tsayawa tare a kan nuna goyo bayansu ga Al'ummar Falasɗinu, da kuma neman bude kan iyakokin kasar, da rusa shingayen da aka Ƙaƙaba masu.
4. Samar da duk wata hanya da za ta taimakawa al'ummar Falasɗinu da gwagwarmayarsu.
YA KU MATASA MASU 'YANCI...!
Yakin "Ambaliyar Al-Aqsa" duk da abinda Mujahidai suka gabatar na Jarumta, wanda ya tsoratar da 'Yan Mamaya, har yanzu ana nan a karon farko ne, kuma 'yan'uwanku suna bukatar duk wata hanya ta taimako daga gareku, kuma fili a bude yake ga duk wani tunani da aiki da za ku iya ba da gudunmawa wajen tallafa wa Mujahidai, kuma ku in Allah ya yarda ma'abota hakanne.
"Kuma a ranar nan, muminai za su yi farin ciki da nasarar Allah."
*Allah ya karbi shahidan mu na qwarai, ya warkar da wadanda suka jikkata, ya kuma ba mu nasara mabayyani.*
Saƙo ne daga 'Yan uwanku:
Ofishin Ayyukan Matasa,
Hamas Islamic Resistance Movement.
Mnnu//Ng0027