@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA GASKE ANNABI (S. A. W. W) YAYI HANI GAME DA HAKA ?
A daidai lokacin da wani ke daukar wani abu a matsayin qanqani wani kuma yakan dauke shi da girma ne. Shi aiki kowanne iri ne, na alkhairi ne ko na sharri ba ya qanqanta, domin matuqar an dawwama ana yinsa zai zama mai girma.
Ba ya halatta ga mutum ya aikata wani abu wanda Allah ko Manzonsa (S. A. W. W) yayi hani dashi, kuma ba ya halatta ka fadi wata magana ka jinginata ga Allah ko AnnabinSa matuqar dai ba shine ya fada ba.
Na ji malamai da yawa na fadin cewa Annabi (S. A. W. W) yayi hani game da yin sallar nafila bayan asubah da la'asar, sai dai a fatawar malaman suna cewa babu laifi mutum ya rama sallar data kubuce masa cikin wadannan lokuta biyu da akayi hani a cikinsu.
To, amma shin da gaske ne Annabi (S. A. W. W) ne yayi wanin sallar nafila cikin wadannan lokuta biyu (2) ko kuma dai qirqira ce irin ta ma'abota qirqira ?
Za mu kawo hadisai biyu a matsayin misali don samun amsar wannan tambaya, kuma domin asan shin Annabi ne yayi wannan hani ko kuma dai qirqiro masa akayi. Amma don gudun tsawaita rubutun za mu taqaita fassarar riwayoyin ne kan gundarin hadisan (MATANI) ba tare da sharhin marubucin ba.
Ga riwayoyin nan kamar haka :
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
«183» حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ مَنِيعٍ حَدَّثَنَا هُشَيْمٌ أَخْبَرَنَا مَنْصُورٌ وَهُوَ ابْنُ زَاذَانَ عَنْ قَتَادَةَ قَالَ أَخْبَرَنَا أَبُو الْعَالِيَةِ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ: سَمِعْتُ غَيْرَ وَاحِدٍ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْهُمْ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ وَكَانَ مِنْ أَحَبِّهِمْ إِلَيَّ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى عَنِ الصَّلاَةِ بَعْدَ الْفَجْرِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ وَعَنِ الصَّلاَةِ بَعْدَ الْعَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ الشَّمْسُ. قَالَ: وَفِي الْبَابِ عَنْ عَلِيٍّ وَابْنِ مَسْعُودٍ وَأَبِي سَعِيدٍ وَعُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ وَأَبِي هُرَيْرَةَ وَابْنِ عُمَرَ وَسَمُرَةَ بْنِ جُنْدَبٍ وَعَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو وَمُعَاذِ بْنِ عَفْرَاءَ وَالصُّنَابِحِيِّ وَلَمْ يَسْمَعْ مِنَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَسَلَمَةَ بْنِ الأَكْوَعِ وَزَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ وَعَائِشَةَ وَكَعْبِ بْنِ مُرَّةَ وَأَبِي أُمَامَةَ وَعَمْرِو بْنِ عَبَسَةَ وَيَعْلَى بْنِ أُمَيَّةَ وَمُعَاوِيَةَ. قَالَ أَبُو عِيسَى: حَدِيثُ ابْنِ عَبَّاسٍ عَنْ عُمَرَ حَدِيثٌ حَسَنٌ صَحِيحٌ. وَهُوَ قَوْلُ أَكْثَرِ الْفُقَهَاءِ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمَنْ بَعْدَهُمْ أَنَّهُمْ كَرِهُوا الصَّلاَةَ بَعْدَ صَلاَةِ الصُّبْحِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ وَبَعْدَ صَلاَةِ الْعَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ الشَّمْسُ وَأَمَّا الصَّلَوَاتُ الْفَوَائِتُ فَلاَ بَأْسَ أَنْ تُقْضَى بَعْدَ الْعَصْرِ وَبَعْدَ الصُّبْحِ. قَالَ عَلِيُّ بْنُ الْمَدِينِيِّ قَالَ يَحْيَى بْنُ سَعِيدٍ قَالَ شُعْبَةُ لَمْ يَسْمَعْ قَتَادَةُ مِنْ أَبِي الْعَالِيَةِ إِلاَّ ثَلاَثَةَ أَشْيَاءَ حَدِيثَ عُمَرَ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى عَنِ الصَّلاَةِ بَعْدَ الْعَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ الشَّمْسُ وَبَعْدَ الصُّبْحِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ وَحَدِيثَ ابْنِ عَبَّاسٍ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((لا يَنْبَغِي لأَحَدٍ أَنْ يَقُولَ أَنَا خَيْرٌ مِنْ يُونُسَ بْنِ مَتَّى)). وَحَدِيثَ عَلِيٍّ: ((الْقُضَاةُ ثَلاَثَةٌ)).
Tirmidhi yace : Ahmad Bn Mani'i ya bamu labari, Hushaimu ya bamu labari, Mansur ya bamu labari (shine Ibn Zazana, daga Qatadata yace : Baban Aliyata ya bamu labari daga Ibn Abbas (R. A) yace :
" Na ji ba daga wajen mutum daya ba daga Sahabban Manzon Allah (S. A. W. W), daga cikinsu akwai : Umar Bn Khaddab, ya kasance shine mafi soyuwarsu a wajena cewa Manzon Allah (S. A. W. W) yayi hani game da yin sallah bayan Alfijr (Asuba) har sai rana ta hudo, da kuma yin sallah bayan La'asar har sai rana ta fadi. "
Yace : A cikin babin daga Aliyu da Ibn Mas'ud da baban Sa'eed da Uqbatu Bn Ameer, da Abu Hurairata da Ibn Umar da Samurata Bn Jundabi, da Abdullahi Bn Amruu, da Mu'azu Bn Afraa'a, da Sunaabiheeyi..................
Ruwaya ta biyu kuma na cewa :
«184» حَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ حَدَّثَنَا جَرِيرٌ عَنْ عَطَاءِ بْنِ السَّائِبِ عَنْ سَعِيدِ بْنِ جُبَيْرٍ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ إِنَّمَا صَلَّى النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الرَّكْعَتَيْنِ بَعْدَ الْعَصْرِ لأَنَّهُ أَتَاهُ مَالٌ فَشَغَلَهُ عَنِ الرَّكْعَتَيْنِ بَعْدَ الظُّهْرِ فَصَلاَّهُمَا بَعْدَ الْعَصْرِ ثُمَّ لَمْ يَعُدْ لَهُمَا. وَفِي الْبَابِ عَنْ عَائِشَةَ وَأُمِّ سَلَمَةَ وَمَيْمُونَةَ وَأَبِي مُوسَى. قَالَ أَبُو عِيسَى: حَدِيثُ ابْنِ عَبَّاسٍ حَدِيثٌ حَسَنٌ. وَقَدْ رَوَى غَيْرُ وَاحِدٍ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ صَلَّى بَعْدَ الْعَصْرِ رَكْعَتَيْنِ. وَهَذَا خِلاَفُ مَا رُوِيَ عَنْهُ أَنَّهُ نَهَى عَنِ الصَّلاَةِ بَعْدَ الْعَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ الشَّمْسُ. وَحَدِيثُ ابْنِ عَبَّاسٍ أَصَحُّ حَيْثُ قَالَ لَمْ يَعُدْ لَهُمَا. وَقَدْ رُوِيَ عَنْ زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ نَحْوُ حَدِيثِ ابْنِ عَبَّاسٍ. وَقَدْ رُوِيَ عَنْ عَائِشَةَ فِي هَذَا الْبَابِ رِوَايَاتٌ رُوِيَ عَنْهَا أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَا دَخَلَ عَلَيْهَا بَعْدَ الْعَصْرِ إِلاَّ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ وَرُوِيَ عَنْهَا عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ نَهَى عَنِ الصَّلاَةِ بَعْدَ الْعَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ الشَّمْسُ وَبَعْدَ الصُّبْحِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ. وَالَّذِي اجْتَمَعَ عَلَيْهِ أَكْثَرُ أَهْلِ الْعِلْمِ عَلَى كَرَاهِيَةِ الصَّلاَةِ بَعْدَ الْعَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ الشَّمْسُ وَبَعْدَ الصُّبْحِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ إِلاَّ مَا اسْتُثْنِيَ مِنْ ذَلِكَ مِثْلُ الصَّلاَةِ بِمَكَّةَ بَعْدَ الْعَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ الشَّمْسُ وَبَعْدَ الصُّبْحِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ بَعْدَ الطَّوَافِ فَقَدْ رُوِيَ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رُخْصَةٌ فِي ذَلِكَ. وَقَدْ قَالَ بِهِ قَوْمٌ مِنْ أَهْلِ الْعِلْمِ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمَنْ بَعْدَهُمْ. وَبِهِ يَقُولُ الشَّافِعِيُّ وَأَحْمَدُ وَإِسْحَاقُ. وَقَدْ كَرِهَ قَوْمٌ مِنْ أَهْلِ الْعِلْمِ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمَنْ بَعْدَهُمُ الصَّلاَةَ بِمَكَّةَ أَيْضًا بَعْدَ الْعَصْرِ وَبَعْدَ الصُّبْحِ. وَبِهِ يَقُولُ سُفْيَانُ الثَّوْرِيُّ وَمَالِكُ بْنُ أَنَسٍ وَبَعْضُ أَهْلِ الْكُوفَةِ.
Qutaibatu ya bamu labari, Jareer ya bamu labari daga Adaa'i Bn Saa'ibi, daga Sa'eed Bn Jubair, daga Ibn Abbas yace :
" Abin sani dai Annabi (S. A. W. W) yayi sallah raka'a biyu (2) bayan La'asar, domin an kawo masa dukiya sai ta shagaltar dashi daga yin sallah (nafila) biyu bayan Azahar, sai ya sallace su bayan La'asar, sannan bai qara komawa zuwa gare su ba. "
A cikin babin daga A'ishata da Ummus-Salamata da Maimunatu da Abu Musa .........
Abu Isah (Tirmidhi) yace hadisin Ibn Abbas kyakkyawa ne.........
(SUNAN TIRMIDHI)
NAZARI
-----------------
Cikin riwayoyin akwai nazarori kamar haka :
(1)- Kamar yadda Ibn Abbas ya nuna bisa dogaronsa da labarin da wasu Sahabbai suka ba shi shine, Annabi (S. A. W. W) yayi hani game da yin sallar nafila bayan sallar La'asar da asuba.
To, idan wannan magana da gaske ne sai muce lalle yin sallar nafila a wadannan lokuta biyu ya haramta, domin aikata abinda Annabi (S. A. W. W) yayi hani a kansa saba masa ne, wanda ya sabawa Annabi kuma Allah ya sabawa kai-tsaye.
(2)- cikin riwaya ta biyu kuma Ibn Abbas ya nuna mana ne cewa lalle Manzon Allah (S.A. W. W) yayi sallar nafila bayan La'asar, sai dai ya yi tane a matsayin ramuwar nafilar Azahar wacce ta kubuce masa bai yi ba. Ita fa sallar nafila ba wajiba bace, amma kuma ace za a ramata cikin lokacin da akayi hanin yin sallah a lokacin ?
(3)- To, idan kuwa ganin dukiya za tasa Annabi (S. A. W. W) ya shagala da aikata abinda yake da muhimmanci wanda ake rama shi, tabbas an nuna mana ne cewa shi (S. A. W. W) na da naqasu (tawaya).
(4)-In har ya tabbata cewa ya aikata haka (yin sallar a lokacin da ya hana) zai zama akwai tufka-da-warwara kenan cikin maganganunsa, kuma zai zama yayi hani kan abu shi kuma ya aikata.
(5)- Lalle ba zai yiwu wadannan riwayoyi biyu su zama ingantattu ba, dole daya ya zama qarya in har daya ya zama gaskiya. Ko dai ya zama asalan bai yi hani ba, ko kuma ya zama bai yi ramuwar sallar nafila a bayan la'asar ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
Baban humaid
Mnnu//Ng0027
14th October, 2023/ 29th Rabi'u-Awwal, 1445