Halascin had salloli biyu (2) ba bisa uzuriba !!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


LOKUTA UKU (3) NE NA SALLOLI WAJIBAI 


Al-Qur'ani ne ma'aunin farko wajen hukunci, sai kuma Hadisi wanda ke fassara shi (Qur'ani). Qur'ani ya ambata mana lokutan sallah, sai Hadisi yazo mana da adadin wadannan salloli wajibai. 


Idan ya zamana anyi su akan wadannan lokuta uku babu wani zargi ko kuma yiwa wani kallon banza na rashin dalili.


Abinda ya jawo wannan rubutu shine maganganun da ake samu cikin 'yan'uwa musulmi da ke zargin junansu na ganin wasu na aikata wani abu na sallah wanda ba daidai ba, ma'ana hada sallah a halin zaman gida ba tare da wani uzuri ba, wato ba a halin tafiya ko tsoro ko kuma ruwa ba. 


Wasu sun tafi kan cewa haramun ne hada sallalo a halin zaman gida in ba tare da wata lalura ba, wannan lalura kuwa shine ruwan sama. 


Allah mai girma da daukaka na cewa :


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" أَقِمِ الصَّلاَةَ لِدُلُوكِ الشَّمْسِ إِلَى غَسَقِ اللَّيْلِ وَقُرْآنَ الْفَجْرِ إِنَّ قُرْآنَ الْفَجْرِ كَانَ مَشْهُوداً ."


" KU TSAIDA SALLAH YAYIN DA RANA TA KARKATA ZUWA GA DUHUN DARE, DA KUMA LOKACIN ALFIJR, LALLE (ita sallar) ALFIJR TA KASANCE WACCE (Mala'ikun dare dana Rana) KE HALARTA (don canjin aiki). "


       (SURATUL-ISRA'I :78)


Manzon Rahma Muhammad (S. A. W. W) ya ambata mana wadannan salloli tare da sunayensu biyar, sai kuma ya rarrabe mana lokacin da za ayi kowacce daga cikinsu. 


Don gudun kada wasu suga kamar wannan rarrabe lokaci zuwa biyar ya sabawa ayar Qur'ani sai ya zama yana hada su cikin lokuta uku a halin tafiya ko tsoro ko kuma zaman gida. 


Wasu sun tafi kan cewa hada wadannan salloli a halin zaman gida na faruwa ne bisa lalura, sai shi (S. A. W. W) ya nuna mana a aikace cewa ba lalura ce kadai ke sa yin hakan ba kamar yadda za mu gani insha Allahu cikin riwayoyin dake biye :


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


                         (1)


330- حَدَّثَنِي عَنْ مَالِك ، عَنْ أَبِي الزُّبَيْرِ الْمَكِّيِّ ، عَنْ سَعِيدِ بْنِ جُبَيْرٍ ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبَّاسٍ ، أَنَّهُ قَالَ : " صَلَّى رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الظُّهْرَ وَالْعَصْرَ جَمِيعًا ، وَالْمَغْرِبَ وَالْعِشَاءَ جَمِيعًا فِي غَيْرِ خَوْفٍ وَلَا سَفَرٍ " . قَالَ مَالِك : أُرَى ذَلِكَ كَانَ فِي مَطَرٍ .


Ya zo cikin littafin Imam Malik cewa : An bani labari daga Malik, daga baban Zubair Al-Makkiy, daga Sa'eed Bn Jubair, daga Abdullahi Bn Abbas cewa ya ce :


" MANZON ALLAH (S. A. W. W) YAYI SALLAR AZAHAR DA LA'ASAR A HADE, DA MAGRIBA DA ISHA'I A HADE BA A HALIN TSORO KO TAFIYA BA. "


Maliku yace : " Ina ganin hakan (ta faru ne)  a halin ruwan (sama). "


(MUWADDA-MALIK, KITABUS-SALAH, BABIN HADA SALLOLI A HALIN ZAMAN GIDA) 


Wannan zato né irin na Imam Malik, amma ba wai ya ji daga Ibn Abbas ne ko wani ba, hukunci kuwa ba a gina shi kan zato. 


Dan kaucewa wannan zato na Maliku sai Ibn Abbas yayi bayani cikin hadisin dake biye. 


                     (2)



«187» حَدَّثَنَا هَنَّادٌ حَدَّثَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ عَنِ الأَعْمَشِ عَنْ حَبِيبِ بْنِ أَبِي ثَابِتٍ عَنْ سَعِيدِ بْنِ جُبَيْرٍ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ جَمَعَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَيْنَ الظُّهْرِ وَالْعَصْرِ وَبَيْنَ الْمَغْرِبِ وَالْعِشَاءِ بِالْمَدِينَةِ مِنْ غَيْرِ خَوْفٍ وَلاَ مَطَرٍ. قَالَ فَقِيلَ لاِبْنِ عَبَّاسٍ مَا أَرَادَ بِذَلِكَ قَالَ أَرَادَ أَنْ لاَ يُحْرِجَ أُمَّتَهُ. وَفِي الْبَابِ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ. قَالَ أَبُو عِيسَى: حَدِيثُ ابْنِ عَبَّاسٍ قَدْ رُوِيَ عَنْهُ مِنْ غَيْرِ وَجْهٍ رَوَاهُ جَابِرُ بْنُ زَيْدٍ وَسَعِيدُ بْنُ جُبَيْرٍ وَعَبْدُ اللَّهِ بْنُ شَقِيقٍ الْعُقَيْلِيُّ. وَقَدْ رُوِيَ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ غَيْرُ هَذَا. "


Abu Isah Al-Tirmidhi yace : Hammaadu ya bamu labari, baban Mu'awiyata ya bamu labari daga A'amashi  daga Habeeb Bn Abiy Thaabitin, daga Sa'idu Bn Jubair, daga Ibn Abbas (R. A) yace :


" MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA HADA TSAKANIN AZAHAR DA LA'ASAR, DA TSAKANIN MAGRIBA DA ISHA'I A MADINAH BA TARE DA TSORO BA KUMA BA TARE DA RUWA BA. "


Yace, sai aka cewa Ibn Abbas : Me (Annabi) ke nufi da hakan (na hada sallolin ba bisa wata lalura)  ba ? Sai (Ibn Abbas) yace :


" YANA NUFIN KADA YA QUNTATAWA AL'UMMARSA CE. "


          (SUNAN-TIRMIDHI)


Bisa wannan riwaya ta biyu za mu iya fahintar cewa wannan tunani ko ko hange na Imam Maliku  bai zo daidai ba, domin ba aji daga bakin mai bada labarin ba, kuma ba ace ruwan sama ne yayi sanadin hada sallolin ba. 


                         (3)



«1667» وَحَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ وَأَبُو كُرَيْبٍ قَالاَ: حَدَّثَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ (ح) وَحَدَّثَنَا أَبُو كُرَيْبٍ وَأَبُو سَعِيدٍ الأَشَجُّ- وَاللَّفْظُ لأَبِي كُرَيْبٍ- قَالاَ: حَدَّثَنَا وَكِيعٌ كِلاَهُمَا عَنِ الأَعْمَشِ عَنْ حَبِيبِ بْنِ أَبِي ثَابِتٍ عَنْ سَعِيدِ بْنِ جُبَيْرٍ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ جَمَعَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَيْنَ الظُّهْرِ وَالْعَصْرِ وَالْمَغْرِبِ وَالْعِشَاءِ بِالْمَدِينَةِ فِي غَيْرِ خَوْفٍ وَلاَ مَطَرٍ. فِي حَدِيثِ وَكِيعٍ قَالَ: قُلْتُ لاِبْنِ عَبَّاسٍ لِمَ فَعَلَ ذَلِكَ قَالَ كَيْ لاَ يُحْرِجَ أُمَّتَهُ. وَفِي حَدِيثِ أَبِي مُعَاوِيَةَ قِيلَ لاِبْنِ عَبَّاسٍ مَا أَرَادَ إِلَى ذَلِكَ قَالَ أَرَادَ أَنْ لاَ يُحْرِجَ أُمَّتَهُ. 


Imam Muslim ya riwaito cewa, Abu Bakrin Bn Abiy Shaibata da baban Kuraib sun bamu labari suka ce : Baban Mu'awiyata ya bamu labari kuma baban Kuraib da baban Sa'eed Al-Ashajju sun bamu labari. A lafazin baban Kuraib suka ce : Waki'i  ya bamu labari dukkansu daga A'amashi daga Habeeb Bn Abiy Thaabit, daga Sa'eed Bn Jubair daga Ibn Abbas (R. A) yace :


" MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA HADA TSAKANIN AZAHAR DA LA'ASAR, DA MAGRIBA DA ISHA'I A MADINAH BA A HALIN TSORO KO RUWA BA. "


A hadisin Waki'i yace : Sai na cewa Ibn Abbas : Don menene ya aikata haka  ? Yace :


" DON KADA YA QUNTATAWA AL'UMMARSA. "


A hadisin baban Mu'awiyata aka cewa Ibn Abbas : Me yake nufi da haka? Yace :


" YANA NUFIN KADA YA QUNTATAWA AL'UMMARSA CE. "


             (Sahihu-Muslim)


Bisa la'akari da riwayoyi biyun saman nan za mu iya cewa babu wani dalili na uzuri da yasa Annabi (S. A. W. W) yayi haka, sai dai kawai don ya nunawa al'ummarsa babu laifi cikin hadawa tunda dama lokuta uku ake dasu. 


                    (4)


«1670» وَحَدَّثَنِي أَبُو الرَّبِيعِ الزَّهْرَانِيُّ حَدَّثَنَا حَمَّادٌ عَنِ الزُّبَيْرِ بْنِ الْخِرِّيتِ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ شَقِيقٍ قَالَ خَطَبَنَا ابْنُ عَبَّاسٍ يَوْمًا بَعْدَ الْعَصْرِ حَتَّى غَرَبَتِ الشَّمْسُ وَبَدَتِ النُّجُومُ وَجَعَلَ النَّاسُ يَقُولُونَ الصَّلاَةَ الصَّلاَةَ- قَالَ- فَجَاءَهُ رَجُلٌ مِنْ بَنِي تَمِيمٍ لاَ يَفْتُرُ وَلاَ يَنْثَنِي الصَّلاَةَ الصَّلاَةَ. فَقَالَ ابْنُ عَبَّاسٍ أَتُعَلِّمُنِي بِالسُّنَّةِ لاَ أُمَّ لَكَ. ثُمَّ قَالَ رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ جَمَعَ بَيْنَ الظُّهْرِ وَالْعَصْرِ وَالْمَغْرِبِ وَالْعِشَاءِ.  قَالَ عَبْدُ اللَّهِ بْنُ شَقِيقٍ فَحَاكَ فِي صَدْرِي مِنْ ذَلِكَ شيء فَأَتَيْتُ أَبَا هُرَيْرَةَ فَسَأَلْتُهُ فَصَدَّقَ مَقَالَتَهُ."


Imam Muslim ya qara da cewa : Abu Rabee'a Az-Zahraaniyyu ya bani labari, Hammad ya bamu labari daga Zubair Bn Khiraiti, daga Abdullahi Bn Shaqeeq yace : 


" Wata rana Ibn Abbas (R. A) yayi mana Khudubah bayan la'asar har rana ta fadi taurari suka bayyana.  Sai mutane suna cewa : " SALLAH  ! SALLAH  !! " Yace : sai wani mutum daga Banu Tameem yazo ko kunya ba ya ji kuma ko togiya (sakaye magana) ba ya yi,  yana cewa : SALLAH  ! SALLAH  !! (suna sanar da Ibn Abbas cewa ya dakata wannan Khuduba tasa domin lokacin sallah ya yi). 


Sai Ibn Abbas (R. A) yace :


" ZA KU SANAR DANI SUNNAH NE  ? (yana qalubatarsu) BABU UWA GARE KA ! "


Sa'an nan yace : " NA GA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA HADA TSAKANIN AZAHAR DA LA'ASAR, DA MAGRIBA DA ISHA'I. "


Sai Abdullahi Bn Shaqeeq yace : " Sai wani abu ya sosa min zuciyata (na bacin rai da rashin yadda da abinda Ibn Abbas ya fada).  Sai na tafi wajen Abu Hurairata na tambaye shi (game da abinda Ibn Abbas ya fada), sai (Abu Hurairata) ya gaskata abinda (Ibn Abbas) ya fada. "

 


      (Sahihu Muslim)


Bisa wadannan riwayoyi za mu iya cewa babu wata hujja dake nuna cewa ruwan sama ne kadai zai iya bada damar hada salloli a halin zaman gida. 


N.B - A lura da kyau, wannan ba wai yana bada lasisin kowanne lokaci ya zama mutum na hada tsakanin wadannan salloli ba, domin ba cewa kowanne lokaci ne Annabi (S. A. W. W) ke yin hakan ba. 



Abinda aka fi sani shine yana rabawa, amma kuma yana hadawa ko ba ruwan sama. Saboda haka in ba jahilci ba babu hujjar zargin wanda aka ga yana hada tsakanin salloli a wasu lokuta kuma cikin halin zaman gida. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)

        Mnnu//Ng0027

3rd Octorber, 2023/  18th Rabi'u-Awwal, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post