DAGA KALAMAN HIKIMA NA IMAM ALI (A. S) !!! (4)


 DAGA KALAMAN HIKIMA NA IMAM ALI (A. S) !!! (4)

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ABIN MAMAKI GA WANDA RAYUWARSA KE QAREWA AMMA BA YA TANADIN LAHIRARSA 

Ya isa abin tunani ga mai hankali ya riqa duban halin da yake ciki na rayuwarsa. Shin, rayuwarsa na qaruwa ne ko kuma raguwa take. 

Idan kasan rayuwarka raguwa dake a kullum, to, ya kamata ka riqa tanadi domin inda ka nufa.

Imam Ali (A. S) na cewa :

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):

 " عَجِبْتُ لِمَنْ يَرى أَنَّهُ يَنْقُصُ كُلَّ يَوْمٍ في نَفْسِه وَ عُمْرِه وَ هُوَ لا يَتَأَهَّبُ لِلْمَوْتِ."

" INA MAMAKI GA WANDA KE GANI A KULLUM RAGUWA YAKE AKAN KANSA DA RAYUWARSA AMMA KUMA SHI BA YA YIN TANADI DOMIN MUTUWA. "

المصدر : عيون الحكم والمواعظ

A wani guri kuma yake cewa :

قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):

 " عَجِبْتُ لِمَنْ عَلِمَ أَنَّهُ مُنْتَقِلٌ عَنْ دُنْياهُ كَيْفَ لا يُحْسِنُ التَّزَوُّدَ لِاخِرَتِه."

" INA MAMAKI GA WANDA YASAN CEWA SHI MAI CIRUWA NE DAGA DUNIYA, TO, TAYAYA BA ZAI KYAUTATA GUZURI DOMIN LAHIRARSA BA ?"

المصدر : عيون الحكم والمواعظ

Tabbas akwai abin mamaki, domin zai zama rashin hankali ko rashin tunani ga mutum ya zama ba ya kyautata gurin tabbatuwarsa, domin ita duniya ba gurin tabbata bace. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

             (08137925034)

6th October, 2023/ 21st Rabi'u-Awwal, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post