@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DUK ABINDA KAKE DA YAQINI A KANSA KA GABATAR DASHI
Addinin muslimci addini ne wanda ke buqatar samun yaqini. Duk abinda kake da yaqini a kansa kada kaji tsoron gabatar dashi.
Ba zai yiwu ka zama kana aikata wani abu na addini wanda ya sabawa fahimtar wasu sannan ace baka fuskanci qalu-bale daga gare su ba.
Saboda haka matuqar kana da yaqini kan wani al'amari, to, ka gabatar dashi kawai ba tare da jin tsoron masu zargi ba. Da ace ana tsoron zargi haqiqa da Annabi (S. A. W. W) ba gabatar da addinin da yazo dashi wanda ya sabawa na larabawa ba.
Imam Ali (A. S) na cewa :
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
قال الإمام علي(ع):
" لا تجعلوا علمكم جهلا و يقينكم شكا إذا علمتم فاعملوا و إذا تيقنتم فأقدموا. "
" KADA KU SANYA ILIMUNKU (ya zama) JAHILCI, KUMA YAQININKU YA ZAMA KOKONTO. IN DAI HAR KUN SANI (abinda kuke kansa daidai ne) KU AIKATA , KUMA IDAN (kuka sami) YAQINI (kan wani al'amari) KU GABATAR (dashi). "
المصدر : بحار الأنوار
Saboda haka mu kasance masu aikata abinda muke da ilimi kansa ko da kuwa ya saba fahimtar wasu. Kuma abinda muke da yaqini a kansa mu dage wajen gabatar da dashi don neman yardar wanda yafi cancanta a nemi yardarsa (Allah).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(0813792503)
Baban humaid Mnnu//Ng0027
4th October, 2023/ 19th Rabi'u-Awwal, 1445.