Ƴan sanda sun kama Naira Marley kan mutuwar Mobhad


Rundunar ƴan sanda a jihar Legas ta ce tana tsare da tauraron waƙoƙin Afrobeats, Naira Marley kan mutuwar tsohon abokin aikinsa Mobhad. Mai magana da yawun rudunar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana haka da yammacin Talata.

Ya ce ''An tsare Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley domin yi masa tambayoyi da sauran ayyukan bincike.'' Tun bayan mutuwar Mobhad a watan Satumba, ƴan Najeriya musamman matasa ke zargin Naira Marley da hannu a lamarin sanadiyyar saɓanin da suka samu kafin raba-gari.

Sai dai Naira Marley ya sha musanta zargin.

Matasa da dama sun gudanar da zanga-zanga a manyan biranen kasar domin neman hukumomi su gudanar da bincike kan lamarin. Hakan ya sa rundunar ƴan sanda ta zakulo gawar Mobhad da niyyar gudanar da bincike don neman gano sanadiyar mutuwar sa.

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post