YANZU YANZU: An ci gaba da cafke matsafa masu shanye wa mutane jînî a Zariya.
Daga Zuhair Ali Ibrahim.
“Wata jita-jitar da ake yaɗa wa a Jihar Kano, da kuma jihar Zamfara da sauran garuruwa na Arewacin Nijeriya kan matsafa masu shanye jînî ta fara bazama a cikin garin Zariya, yanzu haka ankama wata mata tare da ɗan ta da zargin ta shanye wa wani yaro mai tallar gyaɗa jînî kamar yadda jaridar ALFIJIR HAUSA ta samu rahoto. “Wakilin mu ya bibiya lamarin tare da tabbatar da inda abun ya faru, bisani ya samu tabbacin cewa abin lamarin ya faru ne a Sabon Garin Zariya a dai-dai wani wuri da ake kira da „Wurri Street” bisani angarzaya da matar babban cibiyar tsaro ta jami'an tsaron 'yan sanda dake kasuwan mata.”
Bugu da ƙari a jiya talata wani abin al'ajabi ya auku a kasuwar wayoyi ta PZ dake garin Zariya, inda wata tsohuwa ta zo neman taimako gurin daya daga cikin matasan dake sana'a a kasuwar mai suna Sufiyanu, inda bayan ya ba ta sadaka kawai sai ya ji kan sa ya fara sarawa, inda nan take ya yanke jiki ya fadi. “Sakamakon hakan ne abokan sana'ar Safiyanu suka yi gaggawar kamo matar, inda suka sa ta tsallaka shi kusan sau hudu kafin ya tashi zaune amma hannuwansa sun ki yin aiki. Gudun kada mafusata su huce fushin su a kan tsohuwar ne ganin cewa ana shirin dukan ta sai wasu daga cikin su suka kira jami'an 'yan sanda suka tafi da ita.”
Real Naseer Umar Alhassan 0015