YADDA MUZAHARAR TATTAKIN YANKIN KANO YA KASANCE 1445 2023
Real Naseer Umar Alhassan ✍️
To Alhamdulillah da faro ita dai wannan muzaharar ta tattakin yan kano an ɗauko tane daga wani gari da ake kira Dotsa. Antashi da muzaharar ne da misalin karfe 9:00am saura ana ta tafiya ana ta wakokin juyayin Aba Abdullahil Hussain (As) dana su Zainabul Kubra da sauran su a haka haka har aka isa zongon hutawa gaban sabuwar tshar motocin nan da aka bude ta matafiya kudu an isa wurin ne da 1:00am da wani abu. Sai aka dan huta na tsawon wasu awanni aka huta tare da cin Abinci da kuma Sallah.
Bayan tasowa daga zongon hutu sai aka dora da muzaharar da karfe 1:30pm aka ci gaba da abinda ake gabatarwa. Shi wannan tattakin ya hada yan kuna kamar irin su potiskum, Azare, jigawa, Kano, Mai duguri. Sannan acikin sahun muzaharar tattakin akwai rundina rundina wadanda gasu kamar haka farko muzaharar tattakin yan Jaishi Zakazaky (H) ne bayan su kuma sai Hurras Jaishi Amirul Mu'uminin (As), da Hurrus sai tagawagar Wakilan da'irori Hadi da burazu, sai kuma sauran rundinonin suka biyo a bay irin su Jaishi Turi (Ra), Ansaru Zakazaky (H), Kautal ko'e fulani, Siriyyatu Qaseem Sulaimani, Uzairiyya group, Mu'assasatul Shurafa, Rijalu Zakazaky (H), Hurras Enforcement, 'Yan tamsiliya, Jaishi Aliyu Hydar, Intizarul muntazarun, Jaishi Sayyeed Ahmad, 'Yan tauri, Rijalu Sidi Zakazaky (H) sai tawagar Sisters.
Sannan an samar da masu tablig masu yiwa Al'umma bayanin abinda ya muka fito da kuma abinda ya faru da zuriyar gidan Manzon Allah (Saww) kafin akarasa wajan rufewa an hada maukibai wanda Hurras Enforcement sun hada maukib, sai maukib din Jaishi Turi (Ra), sannan sai bangaran Jasas suma sun hada nasu inda suka hada maukib din Sayyeeda Ahmad, maukib din Sayyeed Mahmoud, maukib din Sayyeed Hamid, maukib din Sayyeed Aliyu Hydar, Maukib din Hammad, maukib din Humaid. Wanda daga nan sai filin ruwa.
Hoto Na Shaheeda Bawan Allah
19/2/1445.
5/8/2023