Wafatin Manzon Allah (S) Da Abubuwan Da Su ka Faru!


 Wafatin Manzon Allah (S) Da Abubuwan Da Su ka Faru! 

A shekara ta goma bayan Hijira Manzon Allah (S) yayi wafati! ranar 28 ga watan Safar shekara ta 11 bayan Hijira. Manzon Allah ya aiyana runduna karkashin jagorancin Usama Bini Zaid, wannan rundunar an aiyana ta ne akan suje su yaki rumuwa saboda barazana da suke dashi akan Musulunci, a wannan lokacin ance Manzon Allah (S) ya fara Rashin Lafiya, Annabi ya umarci kowa da kowa yabi usama a matsayin Jagoran su a wannan yaƙin , Iman Ali ne kawai Annabi ya barshi a gida. To a wannan lokacin akai ta ƙananun maganganu har takai da ta dawo kunnen Annabi, a wannan halin Annabi ya fito Masallaci yayi huduba akan kowa yabi Usama har Annabi yana cewa Allah ya tsinewa Wanda yaƙi bin wannan runduna ta Jaishi Usama. Amman duk da wannan ƙarfafawa da Annabi yayi wasu basu bi wannan runduna ba. A wannan lokacin Manzon Allah (S) yana gidan Umusalma sai Aisha ta roki sauran Matan Annabi akan Annabi ya koma ɗakin ta zata shagaltu da kula da jinyarshi, saboda tafi sauran matan Annabi ƙarancin shekaru a lokacin to sai suka amince. Washe gari sai ga Bilal da Asuba yayi Sallama yana tunatar da Annabi lokacin Sallah sai Annabi yace masa to kuje kuyi sallah saboda ni yau ina fama da jiki na a lokacin ne Aisha tace wa Bilal kuce Abubakar yaja Sallah Hafsa ma tace kuce Ummar yaja Sallah sai Annabi yaga wata fitina zata auku haka Annabi ya kama hanun Imam Ali ya fita Masallaci yaja Mutane Sallah bakaman yadda ake cewa Abubakar ne yaja Sallah ba! 

Bayan Annabi ya dawo gida sai yasa aka kira masa Abubakar da Umar da sauran mutanen sai ya tambayesu shin bana umarce ku kubi rundunar Usama ba sai Abubakar yace lallai ni na bisu dawowa nayi saboda na sabunta gani na dakai sai umar yace ni ban fita ba saboda in tsoron yanayin jikin ka! Manzon Allah ya kara jaddadawa Wadannan mutanen cewa kubi rundunar Usama to a lokacin zazzaɓi mai zafi ya kama Annabi har sanda takai ga ya suma! Bayan ya farka sai yace musu Ku bani abin rubutu na rubuta muku abinda inkunyi riko dashi baza ku taba bacewa ba sai Umar yace Alƙur'ani ya ishe mu! (ciwon ya rinjaye shi). Sai Annabi ya bude ido ya kallesu sai sukayi turus wani yace Ya Manzon Allah shin akawo ma abin rubutun da kayi umarninne? Sai Manzon Allah cikin ɓacin rai yace bayan abinda kuka fada duk da haka Annabi saida yace musu na bar muku wasiya akan Iyalan gidana ku rikesu da Alkhairi! Annabi yace duk su tashi su bashi waje, ya rage babu kowa sai kasawan sa kaman su Imam Ali (As) da Abbas banfan Manzon Allah (S).

Ance washe gari jikin Manzon Allah yayi tsanani har ya zamana ba a barin kowa ya shiga wajen Annabi sai Imam Ali shi kadai bayan Annabi ya sami barci sai Imam ya tafi wani Abu da ya shafeshi bayan Annabi ya farka sai yace ku kiramin masoyi na sai Aisha tace ku kira Abubakar bayan Annabi ya ganshi saiya kau da kai, ya kara nuni a kira masa masoyin sa sai Hafsa tace ku kira masa Umar da Annabi ya ganshi ya kawar da kan sa ya kara kira cewa ku kira min Masoyina sai Umusalma tace ku kira masa Aliyu Ɗan Abi Ɗalib shikadai yake nufi bayan Imam Ali yazo sai Annabi ya kirasa yana me cemasa ya kusanto har sanda zufan jikin Annabi tana shafan zufan Imam Ali to a wannan lokacin ne yayi dogon ganawa da Imam Ali bayan haka sai akaji Annabi yana Kalman Shahada wannan shine karshen rayuwar Manzon Allah (S).

A lokacin da ake kokarin shirya Manzon Allah (S) wa su kuma daga Sahabbai suna can suna batun wazai gaji Manzon Allah (S) Dan haka an bar Ahlul Baiti as da wasu wajan shirya shi da kuma yin Sallah a lokacin, sai daga baya mutane suka rika shiga suna yiwa Annabi Sallah ba tare da limami ba. Bayan Imam Ali (As) ya ma Annabi Sallah. Dan haka idan mutum bai fahimci abin da ya faru a karshen rayuwar Manzon Allah ba to bazai iya fahimtar Haƙiƙanin Musulunci ba! Wani Bangare daga cikin jawabin da Sheikh Adamu Ahmad Tsoho ya gabatar a wajen Zaman Juyayin Wafatin Annabi Wanda ya gudana ranar Talata a garin Jos


Alhamdulillah 

#HSZJ 6/October/2021.29/Safar/1443H.

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post