@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MACE BA TA HARAMTA GA MIJI HAR SAI YAYI MATA SAKI UKU A JERE
Rudanin da mutane ke ciki da kuma fatawar da wasu maluma ke bayarwa yasa mu kaga ya kamata muyi wannan taqaitaccen rubutu don haskakawa mutane abinda ya shige musu duhu.
Wasu malaman na yin fatawa cewa ana hada sakin da mutum ya yiwa matarsa kafin ta auri wani da kuma wanda zai yi mata bayan ta auri wani ta dawo wajensa.
Allah (T) na cewa saki sau biyu yake, ko dai a riqa bisa shari'a ko kuma a sallame su da kyautatawa. Ya kuma qara da cewa idan kuma (miji) ya (qara) sakinta bayan biyun da ya aikata, to, ba ta halatta gare shi har sai ta auri wani mijin koma bayansa.
Ma'ana in har aka ce saki uku ya auku tsakanin miji da mata ba ya halatta su qara yin wani aure tsakaninsu har sai ta auri wani sabon miji kuma ya taketa kafin ta halatta ga mijin baya bayan sakin sabon mijin.
Bisa wannan ne wasu malamai ke cewa da ace mutum zai saki matarsa sau biyu sai tayi sabon aure kuma sabon mijin ya saketa ta dawo zuwa ga mijin baya, sai shi ma ya saketa, to, wai za a hada wannan sabon saki dana baya ne, saboda haka ya zama saki uku. Wai babu wani aure a tsakaninsu har sai ta auri sabon miji.
To, gaskiya ba haka hukuncin yake ba, dole sai saki uku ya auku ne a jere ba tare da samun wani shamaki na sabon miji ba.
Bari mu shiga nassi muga hukunci daga wadanda aka ce mu karbi ilimi daga gare su.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
كتاب حسين بن سعيد و النوادر الْحَسَنُ بْنُ مَحْبُوبٍ عَنْ إِسْحَاقَ بْنِ جَرِيرٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: سَأَلَهُ بَعْضُ أَصْحَابِنَا وَ أَنَا حَاضِرٌ عَنْ رَجُلٍ طَلَّقَ امْرَأَتَهُ تَطْلِيقَةً وَاحِدَةً ثُمَّ تَرَكَهَا حَتَّى بَانَتْ مِنْهُ ثُمَّ تَزَوَّجَهَا الزَّوْجُ الْأَوَّلُ قَالَ فَقَالَ نِكَاحٌ جَدِيدٌ وَ طَلَاقٌ جَدِيدٌ لَيْسَ التَّطْلِيقَةُ الْأُولَى بِشَيْءٍ هِيَ عِنْدَهُ عَلَى ثَلَاثِ تَطْلِيقَاتٍ مُتَتَابِعَاتٍ وَ إِنْ كَانَ الْأَخِيرُ لَمْ يَدْخُلْ بِهَا ثُمَّ تَزَوَّجَهَا الْأَوَّلُ فَهِيَ عِنْدَهُ عَلَى تَطْلِيقَةٍ مَاضِيَةٍ وَ بَقِيَتِ اثْنَتَانِ.
Ya zo cikin littafin Hussaini Bn Sa'eed da Nawadir Alhassan Bn Mahbub, daga Ishaqa Bn Jareer, daga Abu Abdullah (À. S) yace :
Sashen Sahabbanmu sun tambaye shi alhali ina gurin game da wani mutum wanda ya yiwa matarsa saki daya (1), sai ya barta har ta ba'intu gare shi (wato tayi idda), sa'an nan ta auri mijin nata na farko (bayan ta auri wani miji ya saketa). (Imam Ja'afar (À. S)) yace :
" SABON AURE NE DA SABON SAKI, SAKIN DA YAYI NA FARKO BA KOMAI BANE À WAJENSA WANDA ZA A LISSAFA SHI CIKIN SAKI UKU À JERE. IDAN KUMA YA ZAMA NA BIYUN (da ya aura ta) BAI SADU DA ITA BA (ya saka ta) SANNAN MIJIN FARKO YA AURE TA, TO, ITA A WAJENSA TANA KAN SAKIN DA YA GABATA, YA RAGE (saura) BIYU (a tsakaninsu). "
فقه الرضا ص 31 و 32.
ABIN LURA
-------------------
Abinda ake nuna mana cikin wannan hadisi shine, in dai shi miji na biyu ya sadu da mace, to, wannan saduwa ya rushe sakin da mijinta na farko yayi mata, idan sabon mijin ya saketa ta koma zuwa ga tsahon miji zai zama tamkar sabon aure ne wanda babu saki tsakani in ba su aukar da sakin bayan kome nata ba.
Amma da zai zama sabon mijin zai saketa bayan aure ba tare da ya sadu da ita ba saboda wani dalili, to, idan ta koma ga mijin farko ya zama akwai saki daya (1) kenan taakaninsu, in ya qara yi sai a lissafa shi kan wanda yayi na farko.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda
Baban Humaid Ma'asumah Nigerian News
(08137925034/08126384470)
25th September, 2023/ 10th Rabi'u-Awwal, 1445.