Najeriya za ta biya kamfanonin jiragen sama bashin da suke bin ta


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci babban bankin ƙasar ya dinga shirya zama da masu harkar sufurin jiragen sama duk bayan wata uku don duba hanyar biyan su bashin kuɗaɗen waje da suke bin ƙasar da ya kai fiye da dala miliyon ɗari shida.A kwanan nan ne gwamnatin Najeriyar ta sasanta da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, bayan ƙasashen biyu sun dakatar da harkar sufurin jiragen sama a tsakanin su.Ministan sufurin Najeriya, Festus Keyamo ya ce "gwamnatin Najeriya ta damu sosai game da matsalolin da ake fuskanta a harkar sufuri, musamman matsalar ƙarancin kuɗaɗen waje, lamarin da ya janyo wa ƙasar wani abu mai kama da kantar biyan bashi, na kuɗaɗen wasu kamfanonin jirgin sama, na maƙuɗan kuɗaɗe da suka kai fiye da dala miliyan ɗari biyar.

Kuma a halin da ake ciki, gwamnatin kasar ta dukufa wajen magance wannan matsala da ke yin tarnaki ga harkar sufurin jiragen sama. Gwamnatin Najeriyar dai ta ce ta yi wani shiri na inganta harkar sufurin jiragen sama a kasar, wanda zai ƙarfafa gwiwar ƴan kasuwa tare da ƙara inganta harkar baki ɗaya. Gwamnatin Najeriyar dai na daukar wadannan matakan ne a lokacin da ƙungiyar da ke kula da sufurin jiragen sama ta duniya ke kokawa game da gazawar gwamnatin Najeriya wajen biyan kamfanonin jiragen ƙasashen waje kuɗinsu da ya kai fiye da dala miliyan dari shida.

Latsa alamar lasifika da ke ƙasa domin sauraron rahoton Ibrahim Isa

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post