Me ka sani game da musibar ranar Alhamis ???
Tarihi ya rabbatar da faruwar wani mummunan al'amari da ya faru a ranar Alhamis ɗin 25 ga watan Safar , shekara ra 11 daga Hijira , wanda bayan kwanaki uku da faruwar wannan al'amari Annabi Muhammad (saww) yayi Shahada .
Mene ne wannan Mummunan al'amari ?
Wata waƙi'a ce da Sahabin Annabi (saww) Abdullahi Ibn Abbas ya siffantata da musibar ranar Alhamis , Ya kasanace in ya tuna da wannan rana yakan jiƙa ƙasa da hawayen rakaici sabida girman abinda aka yi a cikinta !
A wannan rana Annabi (saww) yana kwance a rashin lafiyarsa ta ajali ya nemi abun rubutu don ya rubutawa wannan al'umma wani abu da in sunyi riƙo dashi baza su ɓata ba har abada a bayansa , nan take ɗakin da Annabi (saww) yake kwance ya kaure da rikici da hayaniya , wasu suna a zartar da umarnin Annabi (saww) , wasu lo kuma suna cewa kar ayi abinda ya nema na kawo abun rubutu , har suka siffanta Annabi (saww) da cewa yayi hauka da zancen banza , wanda ya faɗi wannan naganar shine Sahabin Annabi (saww) Umar bin Khaɗɗab , ganin haka Annabi (saww) ya umarcesu da su tashi su bashi wuri don baya halatta ayi jayayya Da Saɓani a inda yake , kamar Yadda Allah yayi yani a cikin Alkur'ani cewa :
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ وَلا تَجْهَرُوا لَهُ بِالْقَوْلِ كَجَهْرِ بَعْضِكُمْ لِبَعْضٍ أَنْ تَحْبَطَ أَعْمَالُكُمْ وَأَنْتُمْ لا تَشْعُرُونَ
[الحجرات:2]
Ibn Abbas yakan yi kuka kamar ransa ta fita idan ya tuna wannan abu yana cewa: Babbar nusiba Itace abinda ya hana Annabi (saww) a rubuta abinda yaso rubutawa a wannan lokaci .Darasi da abun lura da ya wajaba ga kowanne mutum Musulmi msi lafiyayyen tunani ya ɗauka , ya kuma bincika a cikin wannan al'amarin na dayawa daga ciki :
1. Me yasa aka hana Annabi (saww) yayi wannan rubutu tare da ya bayyana manufarsa ta son yin rubutu ?
2. Shin ya hallata wani ya saɓa umarnin Annabi (saww) na daga abinda yaso yi musamman in ya shafi shiryar da al'uma ?
3. Shin ya hallata ga yani ya keta alfarmar Annabi (saww) har takai ga ya siffanta shi da Halinka sa sirinbahana ?
4. Me Manzon Allah (saww) yaso ya rubutawa wannan al'umma wanda in sunyi riƙo dashi bazasu ɓata ba a bayansa ?
5. Shin Annabi (saww) ya rubuta abinda yaso rubutawa daga baya ko bai rubutaba ? Domin ba ta yanda za'ai ace yasan shiriya da tsirar al'umarsa a cikin wannan abu amma yaƙi rubutawa sabida wasu sun dakatar dashi .
6. Menene hukuncin wanda ya saɓa umarnin Annabi (saww) , musamman mummunar saɓawa har ya keta alfarmarsa ?
7. Menene matsayarka game da musibar ranar Alhamis ? Kana tare da yin rubutu watau Annabi (saww) ko kana tare da ƙin yin rubutu ?
لبيك يا رسول الله
Ya Allah muna kawo maka kukan rashin Annabinmu (saww) , da kuma fakuwar Imaminmu (a.j.t.f) da yawaituwar maƙiyanmu da fitintunu a cikinmu ka dubemu .
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Real Naseer Umar Alhassan 0015