Yaudai Wani dan kasuwa a jihar Zamfara ya yayi Abin kiriki ya karya farashin kwanan Masara daga 1,300 zuwa Naira 500 domin saukakawa talakawan jihar.
By Daily News Hausa
A yau Litinin da safe dan kasuwa Alhaji Ahmad Mande Tsafe (Sarkin sudan na Tsafe) dake karamar hukumar Tsafe jihar Zamfara, ya karya farashin Masara da Dawa domin taimakawa talakawan garin.
Inda yake siyar da kwanan Masara Naira 500 madadin 1,300 da 'yan kasuwa suke saidawa. Yana saida Dawa Naira 500 madadin 1,500 da 'yan kasuwa suke saidawa. Tuni daruruwan talakawan garin sun cika gidanshi domin su siya. Muna Addu'ar Allah ya saka mishi da Alkhairi, da sauran 'yan kasuwar da suke taimakon talakawa, duba da halin da al-umma suke ciki a yanzu.
Daga Comr Abba Sani Pantami
Real Naseer Umar Alhassan 0015
Tags:
Labaran Duniya