‘Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Gurku Da Matarsa Wasu 'yan bindiga cikin daren jiya sun yi garkuwa da Mai Martaba Sarkin Gurku, Alhaji Jibril Mamman Waziri dake karamar hukumar Karu, jihar Nasarawa.
'Yan bindigan dauke da bindigu sun kuma yi awon gaba da matar Sarkin, Hajiya Sa'adatu, inda kuma har yanzu babu tabbacin inda suka kai su. Mazauna yankin sun tabbatarwa da Rariya cewa lamarin ya auku ne a daren jiya Lahadi.
Tags:
Labaran Duniya