DAGA KARBALA AL-MUQADDASA:
Yadda al’ummar Karbala (Iraq) ke cigaba da yi wa maziyarta Imam Hussain (A.S) hidima a yau Laraba 13/02/1445 (30/08/2023). A kowane titi ko lungu da saƙo na birnin, maukib-maukib ne inda ake cigaba da yin hidima tare da ciyarwa da shayarwa duk albarkacin Imam Hussain (A.S). Tun satin da ya gabata dai al’ummar musulmi mabiya mazhabar Ahlulbaiti da ma su jin cewa abinda aka yi wa Imam Hussain (A.S) su ma ya shafe su, daga sassan ƙashen duniya dabab-daban, na cigaba da kwarara dan halartar juyayin 40 din Imam Hussain (A.S) na shekarar bana 1445/2023, tare da gudanar da Tattaki daga wasu garuruwan zuwa Karbala.
Ziyarar 40 (Tattaki) ta samo asali ne daga ɗaya daga cikin manyan Sahabban Manzon Allah (S) mai suna Jabir bin Abdullahil Ansari, wanda ya fara yin Tattakin bayan kwana 40 da kisan Imam Hussain (A.S). Jabir ya taka da ƙafarsa har Karbala inda ya yi wanka ya sa turare sannan ya ziyarci ƙabarin Abu Abdullahil Hussain (A.S) da sauran Shahidan da ke tare da shi. Haka kuma Sayyida Zainab ƙanwar Imam Hussain da Imamu Aliyu Zainul Abideen (A.S) sun samu Jabir a muhallin su ma su ka gudanar da ziyarar a tare duk a Karbala. Wannan ya sa ’yan Shi’a da duk wani mai ruhin tausayi na abinda aka yi wa jikan Annabi Imam Hussain (A.S) su ke baro gidajensu dan gudanar da wannan ibada.
Karbala Media Hausa
#وفاء_للثقلين
Real Naseer Umar Alhassan 0015
#وفاء_للحسين
#Arbaeen1445_2023