A daren jiya misalin karfe 7:45pm masu garkuwa da mutane sun shigo cikin unguwar mu tsohuwar kasuwar yan barkono Dandume jihar Katsina suka harbi mutum hudu, Allah yayi wa mutum biyu rasuwa, mace da namiji.
Wadanda Allah Ya yiwa rasuwar ma'auratane kafin sabani ya shiga tsakaninsu su rabo, namijin yazo bikon tsohuwar matar tasa ne, yana tsaye kofar gidansu yana jiran ta fito sabida ta shiga makwafta, fitowar ta ke da wuya bata karasa inda yake ba suka harbe ta, inda harsashin ya fita ya sami yaron da take goye dashi a gefen cikin sa, ita nan take Allah yayi mata rasuwa. Shima tsohon mijin nata kafin yasan mai yake faruwa nan take suka masa harbi uku a kirji da kuma hannusan, harbi na rashin imani, shima nan take Allah yayi masa rasuwa, sai wani bawan Allah shima da suka harba a kafa, yanzu haka yana asibiti shi da wannan yaron da harsashi ya sama dalilin harbin mahaifiyarsa.
Mun ga tashin hankalin da bamu taba gani ba, zuciyar al'umma da dama jiya tayi matukar gizgiza, an karya zuciyar duk wani wanda yake zaune a wannan yanki, al'umma sun shiga rudani, na tabbata a jiya duk wanda kaga yayi bacci wanda ke rayuwa a wannan yanki tabbas saide bacci barawo amma bawai cikin natsuwarsa zai yi sa ba. Wannan kisan da akayi wa yan uwanmu wallahi bazamu yafe ba, ya Allah duk wanda ke da hannu akan wannan mummunar hari da koh wane harin ta'addanci Allah ka wulakanta sa. ~Daga Asim Surajo Dandume.
Real Naseer Umar Alhassan 0015