WANNAN ALAMUN ABIN DA KE FARUWA YANZU, SUNYI A LIBIYA._
_Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
"
..America ta zo ta ambata tace zatayi Amfani da ta'addanci wajen sake kama Africa, to shiyasa kukaga wannan alamun abinda ke faruwa yanzu, sunyi alibiya, bayan lokacin da sukaji ɗagawar larabawa, da ɗagowar misira abin ya furgitasu, sai sukaga suma bari suyi nasu mana, sai sukayi a libiya sukaje suka rugurguza libiya ɗin , suka kashe gaddafi, yanzu babu abinda ke gudana a libiya banda kashe-kashe da faɗa da ƙabilanci tsakanin malisha, da ƙabila, da na wariyar launi, su kuwah suna ɗibar dukiya.
To dama ance libiya da nigeria su suke da mai ɗin da ake ce ma (mai me zaki) (sweet crut) to na libiya na sune. Na Nigeria dama sune tunda suna sa gaula ne su ajiye kullum basu da wani aiki sai su samo wani gaula suce shine shugaban kasa, su samo dolo mataimakinsa, su samo gaɓo su ce shine gwamna, su samo wofi suce shine minista. gasunan....,
Suyita tatsan arziki ɗin, to yanzu kuma sai sukazo da wani salon.
_Sheikh Zakzaky (H) Cikin jawabinsa na mamayar Africa, a shekarun baya.
@Szakzaky's Gallery
13/8/2023
Ma'asumah Nigerian News Update
Mnnu//Ng0027