"Bushewar Zuciya, Itace Mafi Girma a Cikin Bala'i Bayan Kafirci. Akwai Ayyuka Guda 24 Dake Busar Da Zuciya, Wanda SHARI'A Bata Yarda Da Su Ba,
*1 - Mutum Ya Tsaya Akan Zunubi Guda Daya, Yayi Tayi Yana Maimaitawa.
*2 - Tsawon Buri, Mutum Ya Zama Bai Wadata Da Abinda ALLAH Ya Bashi Ba.
*3 - Yawan Fushi, Ba Akan Tafarkin ALLAH Ba.
*4 - Musulmi Ya Riqe Dan'uwansa Musulmi a Zuciya.
*5 - Son Duniya Kota Halin Yaya.
*6 - Son Girma, Cikin Kowane Hali.
*7 - Katsalandan a Harkar Da Ba Ruwanka a Ciki.
*8 - Yawan Dariya, Mutum Ya Zama Kamar Wawa.
*9 - Yawan Zolayar Mutane.
*10 - Jindadi Saboda Abin Duniya, Har Kamanta Da ALLAH Saboda Farin Ciki.
*11 - Baqin Ciki, Yayin Da Jindadi Ya Zo Ya Koma.
*12 - Gafala Ga Barin Zikirin ALLAH.
*13 - Rafkana Ga Barin Tunanin Lahira.
*14 - Barin Yin Tunani Akan Sha'anin Wuta.
*15 - Barin Yin Tunani Akan Sha'anin Aljannah.
*16 - Yawan Yin Firar Banza.
*17 - Yawan Yin Abota Da Wawaye.
*18 - Da Yawan Cin Haram.
*19 - Mugun Cin Abinci.
*20 - Da Yawan Janyo Sha'awa.
*21 - Yawan Barci
*22 - Yawan Tunanin Banza
*23 - Qarancin Ambaton ALLAH
*24 - Ji Da Kai, Ji Da Kai,
ALLAH YA TSARE MANA ZUCIYOYINMU DAGA BUSHEWA ELAHEEEY AMEEEN.
Islam Autar mama:-
Ma'asumah Nigerian News Update, Mnnu//Ng0027