SHAIHK ZAKZAKY YA YIWA HAUSAWA WASU MAGANGANUN MALAM BAHAUAHE GYARA GWARE. RANAR HAUSA TA DUNUYA


1, Malam Bahaushe: So Sone Son Kai Yafi


Sheikh Zakzaky: So So Ne Amma Son Annabi Yafi,


2. Malam Bahaushe: Tsoron Allah A Zuci Yake


Shaikh Zakzaky: Tsoron Allah ba kawai a zuci yake ba, yana danfare ne da aiki, misali; In kana son Budurwa a cikin zuciyarka, sai kawai ka ji Ayyururui an kawo ma Amarya? Ai dole kadan yi kazar-kazar, ka nuna a aikace, kuma ka yi wasu ‘yan sa’ayoyi, to haka nan in kana tsoron Allah, dole a gani aikace a gabobinka.


3. Malam Bahaushe: Wal Bani Wal Baka Wal Hanani Wal kememe


Shaikh Zakzaky: Karin maganar bahaushe da ke cewa; “Wal-Bani Wal-Baka, Wal-Hanani, wal Qememe” ta saɓawa koyarwar addini, Manzon Allah (S) ya koyar da bayarwa hatta ga mai maka rowa ne. Sai dai mu ce; “Wal-Bani Wal-Baka, Wal-Hanani Wal-Baka!”.


4. Malam Bahaushe: Bin Nagaba Bin Allah.


Shaikh Zakzaky: Bin na gaba ba lallai ne ya zama bin Allah ba, Mutane sukance wai bin nagaba bin Allah ne, Eh in na gaban ya bi Allah ba.! Amma in na gaban ya bijirewa Allah, to yi masa tawaye wajibi ne,! Dan haka bin na gaba bin Allah ne idan na gaban ya bi Allah.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post