Haƙiƙanin abun da ya faru bayan soji sunyi ruwan wuta a dabobin Ado Aleru da Gwaska ɗan ƙarami.
Tsaro…..
02/08/2023.
Rundunar Sojin Sama Suna ci Gaba da Luguden Wuta ga Dabobin Yan Bindiga da suka addabi Arewa maso Yamma. A ci gaba da kokarinsu na fatattakar yan ta’adda a dazukan Arewa maso Yamma Rundunar sojin sama tayi luguden wuta a dabobin Yan Bindiga daban daban dake Yankunan Jahar Zamfara da Kuma Jahar Katsina.
Majiya daga rundunar sojojin ta tabbatarwa Jaridar the Nation cewa an kaddamar da Wadannan hare hare ne daga 28 Ga Watan July har zuwa 1 ga Watan August a kananan Hukumomin Zurmi da Tsafe a Zamfara sai kuma Jibia da Faskari dake Jahar Katsina.
Rubdunar sojojin saman sunyi nasarar kashe akalla Yan Bindiga Mutum goma sha shida (16) a Yankin Zurmi Wadanda ake Kyautata zaton masu ansar umurnine daga kasurgumin Dan Ta’addar nan da ya addabi Yankin na Zurmi wanda akafi sani da Dan Karami. Duka a Yankin na Zurmi Majiyar ta tabbatar da sojojin sunyi luguden wuta ga wasu Yan Bindigar kan Mashuna Guda Takwas da suka hango sun koro shanu da ake kyautata zaton satosu sukayi a lokacinda suke tunkarar wata daba tasu inda suke ‘buya.
A wata mai kama da wannan a Yankin Tsafe Shima dake Jahar Zamfara a harin da Sojojin Saman suka kai majiyar ta Jaridar The Nation sun tabbatar da cewa ankaddamar da harin ne a dabar kasurgumin Dan ta’addannan Ado Aleru dake kusa da Tsibirin Asola a yankin na Tsafe inda suka hallaka Yan Bindiga da dama.Wani Mazauni Kusa da Yankin da aka kai samamen Mai Suna Kabiru ya shaidawa Jaridar the Nation cewa sunga wasu Daga Cikin Yan Bindigar da suka tsira da raunuka a wannan harin suna kokarin barin yankin.
Kabiru Ya kara da cewa “ Bayan Kamar awa daya da kai harin ga Yan Ta’addar wasu daga cikin Yan ta’addar sun dawo domin ceton Wadanda sukaji Raunuka tare da tattara saura kayyayyakinsu don barin yanki ananma jirgin ya sake dawowa inda ya kara kai masu hari”
Lokacin da aka tuntubi Mai Magana da yawun rundunar Sojin sama Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da ci gaban da ake samu a yunkurin rundunar na fatattakar Yan Ta’adda inda ya shaidawa Jaridar The Nation Cewa Duka wadannan Hare Harren da ake Kaiwa a Arewa masu yamma suna zuwane karkashin umurnin shugaban sojin Sama Air Marshal Hassan Abubakar na ganin cewa duka Jami’an tsaro sun hada kai da rundunar Sojin sama na ganin an kakka’be yan ta’adda a yankin.
Ubangiji Allah Ka taimaki Jami’an Tsaronmu.Allah ya kawo mana Zaman Lafiya a Yankinmu da Kasarmu baki daya. Ameen
Real Naseer Umar Alhassan 0015