Miji ya karairaya matarsa tare da Yunkurin yanke mata Nono a Zariya


 Miji ya karairaya matarsa tare da Yunkurin yanke mata Nono a Zariya....


Wani matashi mai Suna Abdulkudus Yusuf ya yi ta hanyar Karya mata Hannuwa duka Biyun da kuma daba mata Kwalba a ciki da fuska a garin Zariya dake Jihar Kaduna.


Matashin Wanda tuni Yan Sanda Sun Cika Hannu da shi tare da gurfanar Da shi a kotun Majistare da ke kofar Fada,an zargeshi da yunkurin Hallaka matarsa Sa'adatu Habibu a Anguwar Banzazzau dake birnin Zazzau ta hanyar Balla hannuwanta duka biyun da daba mata Kwalba a ciki,da kuma yunkurinn yanke Nonuwanta da Kwakule mata Ido a wani abu da ake Gani kamar yana da Alaka da Tsafi.


Tuni Kotu karkashin Alkali Baban Ja'e ta tura matashin Gidan Gyaran Hali har zuwa ranar 15 ga watan Agustan nan don Cigaba da Sauraren Shari'ar.


Matar Sa’adatu Habibu,zuwan yanzu tana kwance a asibitin Wusasa dake Zariya, inda take jinyar raunukar da ta samu. Inda tayi kira ga Kungiyoyin kare hakkin dan Adam akan su kawo mata Dauki don ganin an bi mata hakkinta akan mijinta.

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post