Matsayar da Tinubu ya ɗauka na shirin amfani da ƙarfin soji a kan Niger


 Matsayar da Tinubu ya ɗauka na shirin amfani da ƙarfin soji a kan Niger kamar yadda ya rubutawa majalisar dattawa sanarwar shirin afkawa ƙasar ta Niger da yaƙi da sunan kwatowa Bazoum mulkinsa daga mulkin sojin ta Niger anya ba shiryayyen al'alamari ba ne don cimma burin da iyayen gidansu (Amurka da ƙawayenta) suka jima suna hanƙoro a wannan ƙasa tamu mai cike da ma'adanai da sauran albarkatu kuwa?

Eh mana! Ku nazarci lamarin ku gani, yau fa sama da shekaru goma (10) ana fama da matsalar ƴan ta'addan Boko-Haran a wannan ƙasa, ga Kidnappers da kuma Bandits... Me ya hana gwamnati ta shawo kan waɗannan ƴan ta'adda alhali tana da ƙarfin sojin da za ta iya yaƙar wata ƙasa daban? Shin wai yaƙin shi zai kawo mafita ko ƙara yamutsa al'amarin? Niger nada boda da wasu jahohin arewa da suke fama... ko dai ana son karasa kashe al'umman waɗannan yankuna ne ta yadda za a samar da filayen jirajen sama a rinƙa ɗiban dukiyoyi da sunan sulhu a tsakanin Niger da Najeriya? 

#SabonMamayarAfrik

~Repost: Ahmad Awwal

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post