Wadanda kuke kira Malaman addini dana Jami'a , da Manyan mutane, Dattawan kasa, Masana, tsaffin ma'aikata na Sojoji da 'Yansanda har zuwa kan tsaffin Shugabannin kasa, Gwamnoni da Ministoci sun kasa dora Nigeria a tafarkin tsira daga halin bala'i da masifar da take ciki.
Kullum cewa ake yi gara Jiya da Yau, kullum cewa ake yi gara wancan azzalumin da wannan azzalumi, kullum cewa ake yi to wai ina mafita?
Duk tsarin da al'ummar Nigeria suke ganin shi zai fitar dasu daga kangin zalunci sun jarraba amma kullum shiga cikin bala'i suke yi na Jiya dabam na Yau da gobe dabam.
Shi kuwa Malam Zakzaky(H) cewa yayi babu wata mafita idan ba komawa ga tsarin Allahu Ta'ala ba.
Wannan kiran na komawa ga tsarin Allahu Ta'ala Malam Zakzaky(H) ya kwashe shekaru sama da talatin yana kira.
Malam Zakzaky(H) ya sha kamu, dauri, duka, yunkurin kisa da duk wani kokari daga mahukumta na ganin bayansa da da'awarsa.
Malam Zakzaky(H) ya rasa hazikai kuma zakakuran 'Ya:yansa da dubban Almajiransa domin wannan gwagwarmayar ta Tabbatar addinin musulunci a Nigeria ta kai gaci.
Shin akwai wani wanda zai iya gwagwarmaya domin kwatar 'Yancin al'umma a Nigeria kamar yadda Malam Zakzaky(H) yake yi?
Mnnu//Ng0027