IDAN AKA KAWO WA NIJERIYA HARI FARANSA CE BA NIJER BA! IN AKA KAI WA NIJAR HARI AMURKA CE BA NIJERIYA BA!

 


— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Jaddada Kasheji a yayin ganawarsa da Daliban Hauza a ranar Lahadi 13/8/2023 a gidansa da ke Abuja.


Ga bangaren jawabinsa:


“Wannan yana da muhimmanci mutane su san cewa, ba yadda za a yi ace muna fada tsakaninmu da junanmu, da wai wata kasa sunanta Nijar, da wata kasa wai Nijeriya. Dama wa ya yi Nijar da Nijeriyan in ba su ba? Ba su suka tsaga ba? Suka raba kan iyaka suka ce nan Faransa nan Ingilishi? Mu ba mu muka yi ba, dama muna tare, sun gammu kuma a tare ne.


To, abin da nake jin tsoro shi ne, tana iya yiwuwa, tunda yanzu duk sun saka sojoji a kan iyaka, sun yi wata kalma da muka saba jin Amurka tana fada, “all options on the table”. Dama maganarsu ne in suna ma kasashe barazana. Tun Bush uba, da Bush da, da su Clinton da Obama da Trump duk kowannensu ya yi amfani da wannan Kalmar ta “all options on the table”. Sai gashi wannan kalmarsu ce. Wato yanzu ba su cire yiwuwan su kai yaki ba.


To wa zai yaki wani? Don Allah ina ruwan Nijeriya da wani abu wai shi ‘Democracy’ a Nijar? Ina ruwansu? Sau nawa ana juyin mulki a Nijar su koma kan farar hula? Ina ruwan Nijeriya? Nijeriya ta je ta yi musu? Sau nawa kuma ana juyin mulki a nan? Wa ya zo yace mana dole sai an koma farar hula? Na taba jin dirkaniya irin wannan? Haka kawai kace dole kai za ka je ka (yi yaki da sunan kai Damukuradiyya?).


To kuma a sarari yake wannan ba yakinmu ba ne, yakin Amurka da Faransa ne. To kuma Faransa duk da Nijar sun rufe sararin samaniyarsu, sun hana abi, amma Faransa tana bi da jiragenta. Kuma suna da sansanoni na ‘yan ta’adda, wanda har an kama wasu sun je sun kwace su. Daga nan ake kawo hare-hare Nijeriya. Wadanda ake ce ma ‘yan boko Haram din nan, ai sansanoninsu na can ne. Za su zo su kawo hare-hare, su debi gwalagwalai a raba.


To yanzu abin da nake jin tsoro shi ne, suna iya su yi amfani da wadannan ‘yan ta’addan. Ko kuma su da kansu ma su kawo hari ta sama, su ce Nijar ta kawo harin. Sai a fake da wannan ace, ai gashi nan Nijar ta kawo mana hari, saboda haka yanzu Nijeriya ma ta mai da martini. Saboda haka randa duk aka ji ko an yi harbi a Nijeriya, ko an ‘crossing boarder’, to ka tabbatar su ne suka yi; Faransa ce da Amurka suka yi, ba Nijeriya ba, ba Nijar ba!


Ba yadda za a yi ma a yi fada babu ma gaba. Haka kawai? Na wani da nake ba da labarin wani abu da naji wani ya fada, kamar karin magana ne. Yace, wai ko kauye ka je kaga wa da kani suna fada, to ka bincika, Baturen Ingila ya zo wurin. Ingilishi ya zo nan. Yace, saboda duk inda suka je suna hada fada ne. Duk inda suka je, dama salonsu ne, tuntuni haka suka saba, duk inda suka je su hada fada, shikenan, shi wannan ke basu dama su mallaka.


To yanzu, an taba hada fada, baa bin da ya hada mu, muna zaune kawai muna zumunci, mun zama abu daya ne, mu fa ba daban-daban ba ne, mu abu daya ne, kawai rana daya ace wai muna fada? Wannan hauka har ina? To amma suna iya yi, tunda su suke da bukatar yin fada din, su za su iya zuwa su hahharbi wurare, sai su ce kuma ana mai da martani. Sai mu wayi gari kawai ana rugurguza kauyukanmu da biranenmu, ba a san adadin mutanen da za a kashe ba, a kan abin da babu gaira babu dalili illa kawai za su debi arziki. Shikenan abin da ya kawo su, basu kuma damu ba, duk cikanmu gaba daya suna iya kashe kowa, basu kuma damu ba, ba mu ne ke da muhimmanci ba.


Dama da suka fara yakin Ukrain, sun nuna a sarari basu damu da mutanen Ukrain ba, ko da duk za su halaka, suna son a yi ta yakin ne har Rasha ta durkushe. Abin da ya dame su kenan, in ya so duk mutanen Ukrain su halaka. Amma kuma suna takaicin cewa mutanen Ukrain fa Turawa ne, har suna fada, wannan fa ba mutanen wai Afganistan ne ko Iraq ba, mutane ne fa masu shudin ido. Kai ka ji irin wannan. Wato abin takaici, shine mutum mai shudin ido yake mutuwa, inda mutumin Afganistan ne ko mutumin Iraq ai ba damuwa, sai ya mutun kawai. To yanzu kuma ina ga mutumin Afirka, wanda shi basu dauke shi ma a bil’adama ba. Shi kaga shi za a iya kashe shi ba damuwa, in ya so duk gaba daya shi ya kare, tunda shi basu dauke shi ma a matsayin bil’adama ba ma, ballantana har su yi tunanin don me ba zai mutu ba.


To, banda dirkaniya, su wadanda suka yi juyin mulkin nan a Nijar, basu kashe kowa ba, ko an kashe wani? Ko mutum daya. To amma yanzu ana barazanar za a yi amfani da karfin soja a je a yi fada a kashe mutane don a dawo da Bazoum. In mutum yana da hankali, Bazoum din nan yana hannun wane ne? Yana hannun soja. Bazoum din nan fa mutum ne ba tsauni ba ne, kasan in kana rigima kan tsauni idan ka kori mutum sai ka kwace tsaunin ko? Ba kogi ba ne, in kogi ne, idan ka kori mutum sai ka kwace kogin. To shi mutumin nan kuna tsammanin yana hannunsu, sai ku je ku yi musu luguden wuta, sai su ce muku ga Bazoum dinku?


To kuma mu kaddara, in banda wauta ma, idan misali kuka ce Bazoum za ku dawo da, a karagar mulki. To in abin ku je ne, tunda Bazoum din yana nan kamar kila ba za a yi masa komai ba, yana hannunsu. Sai su sako Bazoum din, sai ku dora shi, to za ku dawo Nijeriya ne? Ko kuwa za ku zauna ne ku tabbatar mulkin ya cigaba? Ko kuma yanzu babu wani soja a Nijar kenan sai ku? Na tabbata ba Bazoum ya dame su ba. Abin da ya dame su kawai, su haddasa fitina, a rugurguza kasashen nan guda biyu a debi arzikin wurin. Illa iyaka.


To dama abin da nake jin mana tsoron, kar wata rana a wayi gari an kawo mana hari a ce Nijar ne. In aka kawo mana hari mun san wa ya kawo mana hari, Amerika da Faransa ne, ba Nijar ba! Haka kuma in an kai hari Nijar, to ba Nijeriya ce ta kai mata hari ba, Amurka da Faransa ne! Saboda mene? Ba mu suke bukata ba, basu bukatarmu, suna bukatan arzikin da ke karkashin kafafunmu ne, kuma abin da ya kawo su kenan. Amma muna fatan Allah Ya kiyaye. 


Nace, har wala yau, ba kawai muna gargadin cewa suna iya zuwa su haddasa fada tsakanin abin da suke kira Nijar da abin da suke kira Nijeriya ba ne, suna iya haddasa fada kuma a cikin kowadanne. Yanzu ma suna iya haddasa fada na kabilanci a cikin ita Nijar din, su ce mutanen Bazoum yan kabila kaza ne, mutanen kuma kaza suma kaza, sai a yi fada, kamar yadda suka haddasa a Sudan ana yi tsakanin Dinka da Nuer. To suna iya haddasa wannan.


Kuma Nijeriya din ma, shima suna iya ba da dama ana cikin yin wannan, wani bangare yace shi ma ya balle. An fahimta ai? Sai ya zama shima an koma ana fadan cikin gida a cikin Nijeriya din. Duk zai taimake su. Kowanne zai taimake su. Fadan cikin gida yana iya yiwuwa a cikin Nijeriya kanta, tsakanin Kudu da Arewa, ko Kudu maso Gabas yace ya balle. An fahimta ai? Dama akwai masu kiran balle-balle. Kaga sai a ce a raba kasar gida uku ko hudu. Sannan kuma ko cikin Arewan ma suna iya haddasa rigima, suce ai akwai Musulmi akwai Kirista, an fahimta? Duk suna iya haddawa wadannan, saboda haka a kiyaye.


Musamman ‘yan Nijar. Kar su yarda a jefa su a fadan kabilanci. Domin su al’umma guda ce, kuma kabila Allah ne dai ya yi kabila ba wani ya yi kabila ba. Ko akwai bambancin kabila tsakanin wasu da wasu, Allah ne ya yi kabilolin. Kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa, “Waja’alnaakum shu’uban wa qaba’ila lita’arafu.” Allah ne ya yi kabiloli daban-daban don su san juna, ba don su yi fada ba. Saboda haka yanzu ana iya haddasa wannan, a kiyaye, kar a yarda a fada rigimar cikin gida tsakanin mutumin Nijar da mutumin Nijar da sunan wannan dan kabila kaza ne, wancan dan kabila kaza ne.


Har wala yau, mu kuma nan, kar a haddasa mana rigimar cikin gida tsakanin Kudu da Arewa, ko tsakanin Musulmi da Kirista, ko tsakanin wasu kabila da wasu kabila. Allah dai ya kiyaye.


Abin da muka ce, muna da babban makami, wanda ya fi kowane irin makami, shi ne komawa ga Allah. A koma ga Allah da magiya da addu’a, don duk wata aniya ta makiya Allah Ta’ala ya fi karfinsu. Su karfin nasu na makami ne, amma karfin Allah Ya fi su. Aadawa sun ce “Man ashaddu minna quwwa?” Allah Ta’ala yace, to basu ga wanda ya halicce su ya fi su karfi ba? Yauwa. To Allah Ta’ala ya fi karfinsu. Muna fata Allah Ta’ala Ya kiyaye mu da kiyayewarsa. Insha Allahul Azeem.” 


— Cibiyar Wallafa

Www.cibiyarwallafa.org

Ma'asumah Nigerian News Update

              Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post