Tiyatar yi wa halittar jiki kwaskwarima, abin yayin zamani ne dake ƙara ɗaukar hankulan mata a faɗin duniya, ciki har da ƙasar kamaru.
'Yan mata ne dai aka fi tunanin sune a gaba-gaba wajen rungumar wannan baƙuwar ɗabi'a ta rige-rigen mallakar cikar surar 'ya mace daga dabaru da hikimomin likitoci.
Sai dai, mutuwar wata matashiya a baya-bayan nan cikin yankin Bafoussam, kwanaki ƙalilan da yi mata irin wannan tiyata, ta tayar da hankalin al'umma tare da sake haska girman illolin da tiyatar ke haddasawa,
Kafofin yada labaran Kamaru sun ce an yi wa matashiyar tiyata ne a farkon wannan wata na Agusta, tana muradin a daidaita mata surar damtse da diga-digai da kuma tumbinta, Sai dai tiyatar, ta ya zo da akasi, inda matashiyar ta ce ga garinku nan a ranar Laraba, 16 ga watan Agusta.
Hukumomi dai sun fara gudanar da bincike, kan abin da ya yi sanadin mutuwar Prestige Victoire Kamdem Tiche, wadda aka gano an yi mata ɗinki a sassa da dama na jiki.
Rashin nasarar aikin tiyatar Prestige Victoire, ya zo ne kimanin wata bakwai da mutuwar wasu 'yan mata uku cikin watan disamba a birnin Bafia na lardin tsakiya, su ma bayan an yimusu alluran ƙara cikar mace.
Mata masu yawa ne ke ƙulafucin samun shafaffen ciki da ƙirji hani'an da kuma kuturi fantsam mai sifar ɗaurin kalangu, Kuma akasarinsu Suna koyi ne, da fitattun taurarin fina-finai da mawaƙan zamani.
ko da yake likitoci na gargaɗin cewa irinwannan kwaskwarimar halitta, tana da matuƙar hatsari. mata da yawa awannan zamanin namu kan yi dashe ko gyara don ƙara ciko da zuƙe kitse ko reɗe tsoka daga tumbi ko wani sashen jiki da ba a buƙata, da ƙara girman mazaunai da cinyoyi kai har ma da sharaɓa.
Haka zalika, likitoci na iya tada komaɗar hanci ya Koma ɗan firit, da canza fasalin leɓe ta yadda zai ƙara jan hankali, da raba fuska da kwarmi da taya-ni-munin da ba a buƙata.
A baya dai, masu sha'awar irin waɗannan ayyukan tiyata na tattaki zuwa ƙasashen turai, amma yanzu ana ƙara samun likitoci a cikin gida ko ƙasashe maƙwabta da ke tiyatar kwaskwarimar halitta.
Sedai kumafa a wasu lokutan da wuya a zargi matan da ke tiyatar kwaskwarima don canza fasalin halittar jikinsu sabida wadansu matan a ƙasashe da dama na fuskantar tsangwama, da gori Kai harma da kushen halitta daga ƙawaye ko samari da sauran abokan zama.
Wani masanin halayyar ɗan'adam a Kamaru, ya ce kafofin sadarwa irinsu talbijin da shafukan sada zumunta sun ba da gagarumar gudunmawa wajen sauya wa mata tunani game da yadda suke kallon jikinsu.
Da yake, su mata tun fil'azal, ma'abotan ado da kwalliya ne, ako da yaushe suna duban abubuwan yayi. a cewar, Dr. Didier Demassosso, da mata za su tsaya da iya kyawun da Allah ya yi musu kawai, su yi kwalliya da sanya sutura ta fita-kunya, hakan zai sanya a riƙa ganinsu a matsayin ababen sha'awa.
Ya kuma ce abu ne mai kyau mace ta san cewa idan ba ki da gashin wance, to ki haƙura da yin kitson wance, Sannan mace ta yarda da hakan, kuma ta yi alfahari da yadda Allah ya halicce ta.
Mnnu//Ng0027