duk abinda ya taba nijer zai shafi najeriiya


 DUK ABINDA YA TABA NIJER ZAI SHAFI NIGERIA


Bayan Shugaban Nigeria kuma Shugaban ECOWAS Tinubu ya bayyana tsauraran matakan takunkumi ga Sojojin Nijer wanda suka kifar da Gwamnatin Demokaradiyya, sannan ya ba wa Sojojin wa'adin kwanaki 7 su ajiye mulki imba haka ba Sojojin ECOWAS zasu kaddamar da yaki. Kasar Faransa da Amurka sunce zasu shigo yaki Nijer domin a kori Sojojin da suka kifar da Gwamnatin Muhammad Bazoum. To sai ga sanarwa daga Sojan da ya karbi Mulki a Nijer yana neman agajin Sojojin Rasha, sannan akwai Kasashen Mali da Burkina Faso sunce zasu turo Sojoji Nijer domin su dakile Sojojin ECOWA, to kunga siyasar Turawa ya shigo ciki kenan. Rasha da Amurka zasu zo su jibge miyagun makamai a Nijer, kwatankwacin wanda sukayi a Syria da Libya, daga nan miyagun makamai zasu sake kwarara zuwa Kasashen Afirka ta yamma domin a karfafa kungiyoyin ta'addanci da makami wanda zasu cutar da al'ummah 


Kwanan nan Sojoji sunyi juyin mulki a kasashen Afirka irinsu Mali, Sudan, da Burkina Faso amma ba'ace za'a tura Sojojin ECOWAS ko na African Union su kawar da su ba sai Nijer, to suna da mummunan ajanda ne akan Nijer, saboda Nijer mahadace ta tsakanin Kasashen yammacin Afirka dake sahara.wannan itace ajandar Turawa, zasu sake mamaya a karo na biyu tare da manufar yin mummunan sata na ma'adinan karkashin kasa, shiyasa ban so ECOWAS ta bude kofar yaki ba a Nijer, wannan matsalar sai ta shafi Nigeria sosai.Yanzu haka Fararen hula sun fara nuna goyon bayansu ga Sojojin da suke karbi mulki, Sojojin suna so su yanke alaka ne da Faransa wanda take musu mulkin mallaka irin na zamani, Nijer ta koma alaka da Kasar Rasha. To kun san akwai gaba mai karfi tsakanin Rasha da Amurka, Rasha tana neman hadin kai na Diplomasiyya da Kasashen Afirka da Asia abinda Amurka da Faransa suke gani a matsayin babban kalubale da barazana a garesu Ba ma fatan Yaki a Nijer, Yaki masifa ne, ya zama wajibi ECOWAS tayi taka tsantsan

Allah Ya kiyaye


✍🏻 #youngsoja copied from datti assalafy Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post