DAGA OFISHIN SAYYID IBRAHIM ZAKZAKY (H)



“Tun zamanin Babangida, lokacin ina tsammanin ko 1987 ne ko 1986 ma, an yi rikicin Kafancan a 1987 ne ko? To tun ma kafin 1987 din ne. Akwai wani jami’in tsaro da yake ce min, za mu bata da’awarku. Yace, in mun ga dama za mu iya bata da’awarku. Za mu ce ku kuna kaza, ko kun ce kaza. Wadansu abubuwan da ya farfada basu da dadin ji, yace duk za su iya yi. 


Sai nake ce masa to ku ba da kokari, ai wannan ba zai cuce mu da komai ba, saboda ko ka kwana kana fadin karairayi game da mu, to ai dai muna nan, mu akwai abin da muke fada ko? To, lokacin na ji shi ne kawai, ina ganin abubuwan da suka ce za su yi din. sai yanzu na lura da cewa tuntuni sun dade ma suna yi. 


Sun yi abubuwa daban-daban na kokarin bata da’awa din nan. Akwai mutanen da sukan ta maganganu, musamman mutanen da suke musu ‘Commercial’ din nan, sukan ta miyagun maganganu, su yi ta miyagun maganganu. Don na tuna, a lokacin da nake magana da ‘yan Jami’atul Mustapha a wani lokaci, sai suna fada min, kamar da alama wadannan sun je sun fada musu wasu maganganu, kuma kamar sun hau. Har yana cewa, ya kamata a samu hadin kai tsakanin dukkan dukkan “Jaliyatus Shi’iyya.”


Nace, to kana ta ta cewa “Jaliyatus Shi’iyya”, ni ban san akwai “Jaliyatus Shi’iyya” a inda muke ba, a wajenku an ce muku akwai Jaliyat, amma mu a can inda muke ba mu da wannan “Jaliyat” din. Amma dai akwai Harka Islamiyya, shikenan, akwai kuma wadansu daidaikun mutanen da suke da ra’ayoyinsu daban-daban. Amma wannan sunansu bangare a wajenku. 


To kuma, sai na gaggaya musu, nace to kuma in wadannan mutanen kuke sauraro… Don daga tambayoyin da suke mini, na fahimci an ce musu kaza-kaza. Zan baku misali. Wai ya ake saki? Ya kuke saki? Sai nace, ah, yadda yake a rubuce a littafi. Ai akwai littafin Fiqihu na Ja’afariyya ko? Saki yana nan a rubuce, kuma ka’idar yadda ake yi ake. 


Sai nace musu, amma ni ina da wani ra’ayi wanda ni ba na karanta ba ne a cikin Fiqihun Ja’afariyya, ra’ayina ne na kan fada. Kuma na kan ce ni ba Marja’i ba ne, amma ni da ina da iko, to da ainihin yadda ake daurin aure, haka zan ce a yi saki. Sai a raba goron saki, a tara mutane, ace to ga wane nan shaidan ya hau kansa, zai yi abin da Allah baya so. (Sai ace), to Malam Allah ya sauwake, sai ka fadi wannan mummunan maganar. Sai yace shi wane kaza, ya saki… Sai a rika abin da Bahaushe yake ce ma salati, ace; La’ilaha illallahu Muhammadur Rasullallahi. Har wasu ma su fashe da kuka. Sai yace ya saki matarsa. Shikenan, sai a ce Allah Ya sauwake maka, Allah Ya kiyaye. Sai a ce, sa hannu a takarda, sai ya sa hannu. Nace, ni da ina da iko, zan ce yadda ake taruwa a daura aure, haka za a taru a yi saki. To, amma ban ce muku haka ake yi a littafi ba. 


To da muka yi wannan, sai shi wannan ‘Deputy President’ (Mataimakin shugaban) jami’a din, ya yi shiru, yace min, yadda ka fada din nan, sai ya fadi sunan wani Ayatullah, ya fadi sunansa yace shi ma haka ya fada, ra’ayinsa ne. Yace, ya kamata lallai yadda ake haduwa a yi daurin aure, haka za a hadu a yi saki. To amma ban rike sunan Ayatullah din ba, ya fadi sunansa, yace lallai ra’ayinsa kenan shi ma. An gane?


To, an je an fada musu cewa ga wata hanya ce da muke yin saki. Nasan akwai wani wanda ya zo yace min, wai Malam Turi ya raba shi da matarsa. Wai ya sakar masa matarsa. Nace, ya sakar maka matarka? Yace eh. Sai nace, to tana nan matar? Yace eh. Nace to ka zo min da ita. Ku zo da kai da ita, sai na tambaye ta, in tace tana sonka, zan maida muku da aurenku. To ai ban sake ganinshi ba. Ban sake ganinshi ba, ya tafi kenan. To ta yiwu su irin wannan ne. Na baku misali ne. 


Akwai abubuwan da suke fada daban-daban. Mu muna cewa kaza ne, mu muna kaza ne. Sai nace wa wadannan mutanen, to bari in tare numfashinku, in dai wadannan mutanen ne kuke saurare, suna zuwa suna ce muku mu kaza ne, mu kaza ne, to za su ce muku wane kaza, -suna nufin ni-, yana zuwa saman bakwai ya yi sallah. In dai har za ku saurare su. 


To, sai daga baya, sai suka ce min, ai ma sun fada. Ashe sun ce ma, an ce Malam yana zuwa saman bakwai ne ya yi sallah ya dawo. Sai yace, ai sun fada. Nace ka ji ma, ni a wajena ‘Mubalaga’ na kai, cewa in ma kuka saurare su har wannan ma za su fada muku, ashe har wannan din ma sun fada. 


To, sai na fahimci cewa tunda tuntuni suke cewa, za su fito da wadansu hanyoyi na bata Da’awa, to sai nagano cewa ok, duk aikinsu ne fa. Aikin su ne. Tunda suka ce za su dinga yada abubuwa game da mu. Kuma sun ta yadawa din, sun ta yadawa, har yanzu ma suna yadawa din.


To, ina fadin wannan ne, don ya zama akwai wasu wadanda sukan bushi iska, sai su fadi wadansu maganganu. Wai wani ya yi rubuce-rubuce, wai inda Annabi wane yana da ilimin Malam, wai rabin ilimin Malam, da bai yi kaza ba. Ciki har da Ulul Azmi. Wai inda Annabi kaza yana da ilimin wane, rabin iliminsa ma, da bai yi kaza ba. 


Sai nace to wannan don Allah, shaidana din nan zai yiwu ya fito daga bangaren wani mutum mai hankali? Zai yiwu duk shirinsu ne. Shirye-shiryensu ne, wanda kuma ta yiwu mutum ko dai baqin jahili ne shi, ko yana da tabin hankali. Ka gane ai. Mahaukaci ne shi. Domin ina ganin in dai mutum yana da hankalinsa zai yarda don an bashi kudi, ya rubuta wadannan maganganun? 


To amma, akwai wadansu maganganu da lallai ana biya ne a yi. Don akwai tun lokacin waki’a da aka ce akwai wani, tun muna tsare ne tun 2016, bamu ma shekara a tsare ba, ina tsammanin a watan Afrilu 2016 ne ma. To sai wasu da suka kawo min ziyara, suka cewa, wani ‘blogger’ ya yi rubutu ya yaba ma babban kwamandan sojoji kan aikin da ya yi a Zariya. Ya rubuta.


To cikin wannan watan azumin, sai gashi wasu manyan sojoji sun zo gidansa, suka gaishe shi, suka ce, kai ne wane kaza? Yace eh. Suka ce to ga Ogansu yace a kawo maka wannan don ka yi hidimar sallah. Kuma ka ba da lambar wayarka bayan sallah zai kira ka. Sai aka bashi kudinshi, a lokacin akwai kamar dubu dari biyu (#200,000), aka ce ya yi hidimar sallah. To sannan kuma bayan sallah din aka kira shi aka ce ya zo. Da ya zo kuma har wala yau, aka ba da kunshin da ya nunnunka wannan. Sannan aka fada masa an ji dadin abin da ya rubuta, amma ana son akalla ya samu mutane irinsa kamar guda 20, za a rika biya, su rika irin wannan aiki. An fahimta ai? To, mun san cewa in dai har za ka yi rubutu, za a iya biyanka ka rubuta abin da kake so, ko suka ko wani abu.


Cikin abin da shi wannan jami’in tsaron yake fada min tun a wancan shekarun, ba ina son in fada muku abin da ya fada ba ne, kar in tallata. Amman a ga wasu suna ‘manifesting’ (bayyana) yanzu. Daga ciki akwai cewa, za su kambama shi Malam din, har su nuna shi a wani matsayi, kamar wanda yake ma har mutane za su ce ah abin ko zindikanci ne, ko wani abu mai kamar haka. Nace, ai ba damuwa, ku yi ta yi, ai an ma Annabawa, kuma bai canza Da’awarsu ba. Yace amma za su iya bata abin ai, su maishe shi wani abu daban. Nace za dai ku yi abin da za ku yi, amma ba za ku iya canza Harka ba. To kuma sun ta ta yi din. To sai na lura kamar wannan yana nan, yana daga cikin shirye-shiryensu ne. 


To kuma daga cikin shirye-shiryensu har da cewa, za su rika kambama wasu a cikin Harka din, su nuna su ma ko sun fi Malam, ko su kaza ne. To kuma, kun ga wasu abubuwa da suka jingina ma wasu irin wanda yake Kususiyya ce ma, ba ma ta A’imma kawai ba, akwai wacce take Kususiyya ce ma ta Sahibul Asr Waz Zaman (AJ), amma suka jinginawa wani suka ce kaza ne. Kun ga irin wadannan maganganun, ire-irensu gasu nan, yana daga cikin duk ayyukansu na kurdowa a yi barna. Kuma ba mu kadai suke yi ma ba, suna yin ma kowane ne, amma dai ina magana ne dangane da abin da ya shafe mu.


To, har wala yau kuma, banda kambamawa, ka san hanya biyu ne; da suka da kambamawa. Wannan zai bayyana a matsayin shi mabiyi ne mai Iklasi, saboda haka shi yana daukaka daraja ne. Nan kuwa alhali yana bata Shahasiyya ne. An fahimta ai? Yana bata Shaksiyya ne. Ko kuma ya bayyana a matsayin shi mai suka ne kai tsaye. Gara ma mai sukan ta waje, amma zai yi sharrance-sharrance. Suna sharri iri-iri, miyagun sharrance-sharrance. 


To shikenan nan, kamar yadda kuka ce, ku kanku kun ma wani raddi, wanda shi ‘Bahis’ ne, amma abin takaici bai bi ka’idojin ‘Bahas’ dinsa ba, sai ya saurari abin da wadansu suka bashi kuma ya rubuta a matsayin bincike. Kaga ba bincike ya yi ba kenan. Wannan kawai abin da ya kamata yace, ba ‘Bahas’ na yi ba, wasu ne suka fada min kaza. Amma mai bahasi ai ya kamata ya zama, duk abin da aka fada masa, sai ya bincika. Ko ba haka ba ne? Shi ne ‘Bahas’ ai. 


“Bahas Ilmiy.” Ainihin za ka bincika ne. Maganar Amirulmuminin (AS), yace tsakanin karya da gaskiya, yatsu hudu ne. Sai ya dauki yatsunsa masu albarka guda hudu ya sa a kuncinsa na dama, ya yi haka, yace, gaskiya na gani, karya na ji. Wato tsakanin ido da kunne yatsu hudu ne, ko ba a lura ba? Yace, to gaskiya na gani, karya na ji. Wannan hikima ce ta Amirulmuminin (AS). Ba duk abin da ka ji ne karya ba. An fahimta ai. Wani lokaci kana iya jin gaskiya. Amma me? Za ka bincika ne ka ga ya yake? In aka fada maka, me ya kamata ka yi? Ka bincika. To ka ga bincikawar nan, to ba kuma na ji ba ne shi ma, sai kuma na gani ai ko? Ko ba a gane ba? Na ji, na gani.


Ya kamata ‘Bahis’ ya nuna cewa, Bahasinsa ba an fada masa abu ne kawai ya dauka ya rubuta ba, a’a ya bincika ne ya ga haka nan ne, shi da kansa ya gani. Musamman ma in kana magana kana bin da yake ‘waqi’an’ akwai shi. In Tarihi ne ma, sai ka kawo duk ‘Majmu’an’ abin da aka rubuta dangane da abin, sannan ka kwatanta, ka ga da mai suka da mai yabo, a tsakankani za ka ga wane ne mai gaskiya a cikinsu. An fahimta ai. In ma na Tarihi kenan. Ballantana abin da yake ‘waqi’an’ akwai shi. Kana iya tabbatarwa da bincikawa.


Wato, ina fadin wannan ne, don yanzu na ga wasu abubuwa sun fara fitowa irin wannan. Wasu barna da sunan yabo. Ana so a shuka barna ne, amma sai a bullo da unwanin yabo. To kuma tana iya yiwuwa a ja hankalin wani, wanda shi kuma shi ya dauka ko da gaske ne. Tana iya yiwuwa. Ka san mutane iri-iri ne, ka san ana ‘dealing’ da mutane iri-iri, wasu akwai jahilci wasu akwai wauta. Saboda haka wasu suna iya yi ma da wauta.


Kamar rubuce-rubucen nan da ake yi, yanzu kowa ya zama rediyo da Talabijin din kansa, kowa sai ya fadi abin da ya ga dama, ko ya rubuta abin da ya ga dama. Saboda haka irin wanna hanyar ‘social media’ din yana da hadari sosan gaske. Ba wai duk abin da ka gani ne haka nan ne ba. Wani za ka ga ma da ji ma kasan ana karya ne, amma wasu tunda baka sani ba, kila ka dauka gaskiya ne. Shi yasa ma in ka ga abu, kar ka yi gaggawan karaswa.


Ina tsaren nan, wani yake bani labarin wani Lakcara, ya yi ma dalibansa wata magana, yace ina son don ku gane yadda ‘social media’ yake. Sai ya kira wani dalibi, sai ya yi masa wata magana a kunne, sai yace to ya je ya fada wa na gaba shima a kunnensa, shima ya fadawa wannan. Sai aka zagaya, kowa yana fadan abin da ya ji, har aka zo karshe. Sai aka ce, na karshe ya yi magana. Sai ya fada, sai gashi ba shi ne abin da ya fada ba na farkon. 


Shi abin da yace, shi ne, hukumar jami’ar nan ta samu labarin dalibai za su yi ‘demonstration’ ranar kaza, saboda haka, tana shirin za ta kulle jami’ar tun kafin lokacin. To mutum na karshe, yace, za a yi gagarumin musiba da bala’i a cikin jami’an nan. Yace, to kun ga dai karshe (abin da maganar ta zama), za a yi ‘violence’ yace. Za a yi ‘violence’ a jami’ar nan. Yace, kun ga abin da nake so ku fahimta kenan. Kun ga ga abin da na fada, kuma kun ji na karshe. 


Saboda haka, wannan ya fada, wannan ya fada. Kar ka dauka in ka ga wani abu a ‘social media’ yana nufin da gaske ne. Saboda ko da ma asalin maganar ga yadda yake ne, to karshenta yadda za ka ji shi daban ne. To kar ka gasgata duk abin da kake ji, saboda mutane suna magana daban-daban. Ka gane ai. Saboda haka, tunda yake yanzu zamanin da kowa yake magana ne. Amma yana da kyau haka nan, tunda akwai hanyar da za a iya raddi, tunda ba komai ne bashi da kyau ba ai. Idan mutum ya yi abin nan, yin raddi yana da kyau.


Kwanakin baya na dan yi ma ‘yan uwa (bayani) dangane da maganar raddi, nake cewa, kuma raddi yana bukatar a yi shi da hikima da ilimi. Kuma mutum daya in ya yi ya ma wadatar. In ma ya wadatar muka ji wani ya yi wani abu, aka yi masa raddi na ilimi da hikima shikenan ya wadatar, ba kuma sai kowa shima ya yi raddin ba. Don ainihin sukan so su bamu aiki, yamu-yamu, ya zama bamu da wani aiki sai in an soke mu mu cafe. 


Har nace amma ba ina cewa kar a rama suka ba ne. Wani lokaci suka in zai yi tasiri ne ake magana a kai, in ba zai yi ba kuma ana mantawa da shi ne. Sai na basu misali da cewa, kun ga Allah Ta’ala ya kare Annabi (S) akan abin da suka ce, inda suka ce “Waqalu ma li hazar Rasuli ya’akulud da’ama, wa yamshi fil aswaq.” Wato wannan wai suka ne. Ka san su masu sukan abin da suke nufi? Shi ba Annabi ba ne, tunda yana cin abinci. 


Magana ta fita fes. Mutum ya ji yace, kai wannan gaskiya ne, daga Allah Ta’ala. Sai wani yace af, to ai yana cin abinci. Yana cin abinci? To ashe ma ba Annabi ba ne. To, don Allah ance maka Annabi baya cin abinci ne? A ina aka ce? To wannan yasa ya zama suka. Amma kaga Allah Ta’ala ya yi musu raddi. Yace, bamu taba aiko Annabi ba, face yana cin abinci, kuma yana zuwa kasuwa. 


Wato kaga zai yi tasiri ne. In magana zai yi tasiri ne ake raddi, amma akwai maganar da bata da tasiri sam. Saboda haka, idan aka bamu aikin raddi, bamu da wani aiki sai radde-radde. Za ka ji maganganu iri-iri ana yadawa. Ba kowanne ne ake masa raddi ba, sai wanda zai yi tasiri. Musamman in ya fito daga bakin wani mutum, kamar wanda ya kamata ace shi za a iya jin magana daga gare shi, kuma mutane su gasgata. 


To shi in ya yi wani abu ba daidai ba, to sai a yi masa nasiha a nuna cewa bah aka bane, da hikima. Ba irin yadda wadannan masu zage-zagen (suke yi) ba. Ba zagi, da hikima da ilimi, sai a nuna masa wannan maganar da ya yi ta yiwu shi haka aka gaya masa, a yi masa uzuri, ta yiwu haka aka fada masa, amma abin ba haka ba ne, ga yadda ya ke. Kaga shi kansa in ya karanta zai ga nasiha aka yi masa. Ba za a dira a kanshi ne ba, kamar wasu ma basu iya raddi ba, sai su dira a kan Shahasiyya.


In mutum ya fadi wani ra’ayi ba daidai ba, ba ruwanka da shi wane ne. Ina ganin wasu suna rubutu na zagi, suce wannan dan kaza ne, ko a zagi uban mutum. To ina ruwanka da ubansa, ko uwarsa, ko garinsu, ko kabilarsu? Ka gane? Ya yi magana ba daidai ba, kace wannan abin da ya fada, ta yiwu haka aka fada masa, amma ba haka ba ne. Ko ba a lura ba? Amma baka da bukatar kace masa, ai dama shi kaza ne. Ai dama kaza-kaza. To kaga ka koma kan Shahasiyyarsa. Abin da wasu suke yi kenan.


Kar a koma ga Shahasiyyar mutum, kar a ce masa ma jahili. Ko da abin da ya fada ba daidai ba ne, ba sai a ce masa shi jahili ne ba, don in aka ce masa shi jahili ne, kaga kamar an zage shi kenan. Sai a nuna cewa, tana iya yiwuwa haka shi ya karanta, ko haka aka fada masa, amma ba haka ba ne, ga abin yadda yake. Ko? An fahimta ai. Amma in kace masa, ai jahili ne, kaga ka zage shi. To yanzu kuma ba zai saurare ka ba, shima zai antayo wadansu abubuwa kenan. To kuma dama abin da makiya suke so kenan.”


- Bangaren jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ga daliban Hauzozi a yayin da suka ziyarce shi a gidansa da ke Abuja, ranar Lahadi 26 ga Muharram 1445 (13/8/2023).


@SZakzakyOffice

14/08/2023

Ma'asumah Nigerian News Update

           Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post