ANKARARWA DA JAN HANKALI



Akwai babban abun mamaki da alamar tambaya dangane da abunda ya faru a wannan waki'ar ta Ashura a Abuja, satin da ya gabata. Ni ganau ne kan abunda ya faru. Sojoji ne mota biyar suka rako Muzaharan tun farko har karshenta, amman daga karshe basu afkamata ba, sai suka koma (aikin jarida ma) daukar hotuna da video, a lokacin da yan sanda ke afkama Muzaharar.


Anya? Masu hikima na cewa amfanin tarihi shi ne daukar darasi daga tarihin. Yan uwa za su iya tuna shigen abunda ya faru a waki'ar Buhari; lokaci daya muka ga soja ya zama dan jarida da camera yana daukan video. Kuma suka bayyana ana maganar hankali da su, sabanin yanda aka San sojan Nigeria. Daga karshe meyafaru? Ashe wasan kwaikwayo ne suke shiryawa domin afka muna. 


Yan uwa za su tuna yanda suka yi amfani da salo na harzukawa; yanda suka jibge Sojoji a gaban Hussainiyya, jim kadan aka janyesu. Ana cikin haka ne tawagar sojojin suka iso, suna zuwa suka tsaya da Kansu, ba ma tare da an tare masu hanya ba. 


Na biyu kuma suka yi amfani da ma'aikatansu da ke cikin yan uwa, suka  canza yanayin wurin, wannan ya basu damar iya daukar wannan video din da suka dinga yakar harka da shi. 


Bayan wannan wasan kwaikwayon, har wa yau, sun shiga marhala ta biyu; yan uwa za su iya tuna girman media propoganda da suka kaddamar ga harka a wannan lokacin. Sun dinga promoting wannan video na drama din a cikin alumma ba dare ba rana. A gidajen tv sai da ya zama abun nunawa kullum yaumin. A social media uwa uba, ba inda video din nan bai zaga ba. 


Bayan haka, sun yanko wasu jawaban Jagora (H), tare da hada shi da wasu faretin harisawa, duk domin me? Domin su nuna harka a wata kama da zai kore ma yan uwa kowane kalar nau'i na tausayawa a cikin alumma. 


A wannan gabar, na san yan uwa za su iya tuna girman wahalar da aka sha domin warware wannan shubuhar da aka dasa a kwakwalen alumma game da harka ta hanyar wannan propoganda din. 


Ya zo a hadisi cewa, ba a cizon mumini a rami daya har sau biyu! 

Ma'asumah Nigerian News Update, Mnnu//Ng0027




Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post