Dole ne mutanen da suka wulakanta Al-Kur'ani su fuskanci hukunci mai tsanani - Ayatollah Ali Khamenei
Jagoran addini na ƙasar Iran Ayatullah Ali Khamenei ya bayyana a yau cewa ya zama wajibi mutanen da suka wulakanta Al-Kur'ani mai tsarki su fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya kuma buƙaci ƙasar Sweden da ta miƙa waɗannan mutanen domin yi musu shari'a a ƙasashen musulmi, kamar yadda kafar yaɗa labaran Iran ta ruwaito.
"Dukkan malaman Musulunci sun yi ittifaqi kan cewa waɗanda suka wulakanta Al-Kur'ani sun cancanci hukunci mafi tsauri...Hakkin da ke kan wannan gwamnati ta kasar Sweden shi ne miƙa masu laifin zuwa ga ƙasashen musulmi," in Sayyed ji Khamenei.
Malamai sun bukaci a kashe wata yarinya da ake kyautata zaton ta zagi Annabi Muhammad SAW.
Baban Humaid Ma'asumah Nigerian News Update. Mnnu//Ng0027