☏+2348037538596
Wannan tambaya an dad’e ana kaiwa da kawowa a kanta,
masana da yawa sun tattauna domin ganin sun samar da
ma’anarta domin a gane ta a kuma fahimce ta. Kamar
haka:
Soyayya ita ce nuna ‘kauna daga 6angarori biyu na masu
‘kaunar juna.
‘Soyayya ita ce ni’ima mafi d’aukaka da Allah Ya ba wa
bayinsa. Soyayya ita ce zuciyoyi biyu a dun’kule su cure, su
game cikin zuciya d’aya.
Haka kuma soyayya ita ce rai biyu cikin jiki d’aya. Soyayya
ita ce mutum biyu cikin mutum d’aya. Abin da ake nufi a
nan shi ne, idan mutum ya so wani tsananin soyayya sai ya
zama cewa koda yaushe cikin tunaninsa yake, ba ya
damuwa da kowa sai shi, ba ya son ji da ganin kowa sai
shi, wato kenan sun zama mutum d’aya cikin jiki biyu.’
Duk da abubuwan da muka ambata hakan ba zai sanya mu
ce mun bayyana ha’ki’kanin ma’anar soyayya ba. Domin
ita soyayya ba za a iya siffanta yadda take ba. Sai mutum
ya shige ta, sannan zai san ta.
Baban Humaid. Mnnu/Ng0027, Ma'asumah Nigerian News Update