Akwai Hadisai da dama da suka yi magana a kan
martabobi da darajojin Ahlul Baiti. Za mu takaita
kan wasu hadissai ingantattu guda bakwai (7).
Amma bari mu soma da waɗannan guda biyu
waɗanda suke bayyana fifikon dangin Annabi
(Sallalahu Alaihi Wasallam) baki ɗaya akan sauran
mutane.
Tirmizi ya rawaito falalar Annabi (Sallalahu Alaihi wa'alihi
Wasallam) cewa: Abbas (Allah ya ƙara masa
yarda) ya ce: “Na ce wa Manzon Allah (Sallalahu
Alaihi wa'alihi Wasallam), Ƙuraishawa sun zauna suna bitar
tarihin gidansu. Sai suka kwatantaka da muruccin
kan dutse. Sai Annabi (Sallalahu Alaihi wa'alihi Wasallam)
ya ce: “Da Allah ya tashi samar da halitta, sai ya
zabi mafi alherinta ya sanyo ni a ciki. Ya kuma zabi
mafi alherin ƙabilu ya sanyo ni a ciki. Ya kuma zabi
mafi alherin gidaje ya sanyo ni a ciki. Saboda haka
ni ne mafi alherinsu ga tushe da asali”
Zamu cigaba insha allah...1
Mnnu/Ng0027 Baban Humaid Ma'asumah tv Nigerian News Update