Martabobi da darajojin manzon Allah
Hadisi na
biyu da ya da
a fili, shi ne:
Imamul Muslimu ya ruwaito daga Wasilatu dan
Aska’u wanda ya ce: “Na ji Manzon Allah
(Sallalahu Alaihi wa'alihi Wasallam) na cewa: “Haƙiƙa Allah
ya zaɓi kinanata daga cikin ‘ya’yan Isma’il. Daga
cikin Ƙuraishawa kuma ya zaɓi Banu Hashim.
Daga cikin Banu Hashim kuma ya zave ni”. Muna
iya lura daga wadannan hadisai guda biyu cewa,
Manzon Allah (Sallalahu Alaihi wa'alihi Wasallam) an zabo
shine daga dangi zababbbu.
Don haka, duk wanda ya ke tunanin ya san darajar
Manzon Allah (Sallalahu Alaihi wa'alihi Wasallam) amma
bai san darajar danginsa ba, to bai gano asalin
Manzon Allah ba. Haka kuma za mu iya lura cewa,
Manzon Allah (Sallalahu Alaihi wa'alihi Wasallam) ya na
kula da zumunci na kusa da na nesa, ya na yi mu
su addu’a, kuma ya na yi wa musulmai wasicci da
su kaunace su, su kula masa da su, su kyautata a
matsayin wani haƙƙinsa a kan su...2